Babbar Magana: 'Yan Acaba za Su Yi Fito na Fito da 'Yan Sanda, Hukuma Ta Yi Gargadi
- Rundunar ‘yan sandan FCT ta ce tana da bayanan da ke nuna cewa 'yan acaba sun shirya kai hari kan jami’an tsaro a Kubwa
- ‘Yan sanda sun ce duk wanda ya shiga cikin wannan shiri ko ya tallafa masa da hannu ko baki zai fuskanci hukunci mai tsanani
- An umurci mazauna Abuja da su kwantar da hankalinsu yayin da aka kara yawan jami’an tsaro a yankin domin hana rikici
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan birnin tarayya ta fitar da wata sanarwa tana gargaɗi ga masu babur da ke shirin kai hari kan jami’an tsaro a yankin Kubwa ranar Juma’a, 11 ga Yuli, 2025.
Rundunar ta ce ta samu wani saƙon murya da ke yawo a kafafen sada zumunta, wanda ke zargin cewa wasu ‘yan acaba na shirin tayar da tarzoma.

Kara karanta wannan
Plateau: Batun kisan ƴan Zaria ya dawo, an gurfanar da mutum 22 bayan gama bincike

Source: Facebook
Sanarwar ta fito ne a wani sako da 'yan sanda suka wallafa a X ta bakin jami’ar hulɗa da jama’a ta rundunar, SP Josephine Adeh.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
SP Josephine Adeh ta ce wannan yunkuri na da hatsari kuma ya sabawa doka, kuma duk wanda aka samu da hannu a ciki za a hukunta shi bisa ƙa’ida.
An yi gargadi ga 'yan acaba a Abuja
Rundunar ‘yan sanda ta bayyana cewa ba za a lamunci duk wani yunkuri na kai hari ko tayar da hankali da gangan a FCT ba.
Sanarwar ta ce:
“Duk wanda ya shiga, ya shirya, ko ya ƙarfafa irin wannan yunƙuri da wani dalili, an gargaɗe shi da ya fasa hakan nan take.
"Rundunar za ta ɗauki matakin kama su tare da gurfanar da su,”
Ta ƙara da cewa rundunar tana da karfi da ƙudurin kare jami’anta da kuma tabbatar da zaman lafiya a ko’ina cikin Abuja.
Za a ƙara yawan 'yan sanda a Kubwa
A cewar Adeh, a matsayin matakin rigakafi, mazauna yankin Kubwa za su fara ganin ƙarin jami’an tsaro da motocin sintiri daga ranar Juma’a.
Ta ce hakan ba yana nufin akwai wata matsala ba, sai dai matakin na hana rikici tun kafin ya faru
“Wannan ba barazana ba ce, amma tabbaci ne cewa za mu kare rayuka, dukiyoyi da jami’an gwamnati,”
In ji ta.

Source: Facebook
Shawarin 'yan sanda ga mazauna Abuja
‘Yan sanda sun shawarci mazauna FCT da su ci gaba da harkokinsu ba tare da tsoro ba, su kuma hanzarta kai rahoto idan sun ga wani abu da ke da alamar barazana.
Lambobin kai rahoto da aka bayar su ne:
- 0803 200 3913
- 0806 158 1938
Adeh ta ce rundunar FCT ba za ta yi ƙasa a guiwa ba wajen ganin cewa babu wata kungiya ko mutum da zai tayar da fitina a babban birnin Najeriya.
'Yan sanda sun gurfanar da mutum 22 a Filato
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan jihar Filato ta gurfanar da mutum 22 da aka kama bisa zargin kashe matafiya.
Ana zargin mutanen ne da kashe wasu 'yan jihar Kaduna da suka fito daga Zariya zuwa Filato daurin aure.
Rundunar 'yan sandan jihar ta bayyana cewa za ta tabbatar an yi adalci a shari'ar tare da hukunta wanda aka samu da laifi.
Asali: Legit.ng

