El Rufai Ya Ajiye Adawa, Ya Yi Nasiha ga Mutanen Gwamnatin Tinuhu

El Rufai Ya Ajiye Adawa, Ya Yi Nasiha ga Mutanen Gwamnatin Tinuhu

  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir ElcRufai ya samu halartar wajen ƙaddamar da littafin tsohon ministan shari'a, Mohammed Bello Adoke
  • El-Rufai ya jawo hankalin masu riƙe da muƙami a gwamnati kan cewa watarana za su bar kujerunsu
  • Tsohon gwamnan ya kuma yi kalamai kan muhimmancin littafin wanda Mohammed Bello Adoke ya rubuta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya ja hankalin waɗanda ke cikin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Nasir El-Rufai ya buƙace su da su kasance masu tunanin gaba, yana mai jaddada cewa wata rana za su bar mulki.

El-Rufai ya ba da shawara ga mutanen Tinubu
El Rufai ya shawarci masu mukami a gwamnatin Tinubu Hoto: @elrufai, @DOlusegun
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ce El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis, yayin ƙaddamar da littafi mai suna “OPL245: The Inside Story of the $1.3b Nigerian Oil Bloc”.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon antoni janar na tarayya kuma ministan shari’a a zamanin Shugaba Goodluck Jonathan, Mohammed Bello Adoke (SAN), ya rubuta littafin.

Kara karanta wannan

Jonathan: Abin da ya faru da 'shugaban ƙasa' ya yi yunƙurin tsige gwamnan jihar Borno

Wace shawara El-Rufai ya ba da?

El-Rufai ya ce irin waɗannan littattafan na da matuƙar muhimmanci, ba wai kawai domin gyara tarihi da fayyace gaskiya ba, har ma don ƙarfafa al’adar rubuta tarihin aiki a cikin rayuwar hidima ga ƙasa.

"Ba ma yin hakan yadda ya kamata a wannan ƙasa."
"Ina roƙon waɗanda ke kan karagar mulki a yau da su tuna cewa, nasu lokacin zai zo. Lokacin kowa yana zuwa.”

- Nasir El-Rufai

El-Rufai ya yi magana kan littafin Adoke

El-Rufai ya bayyana cewa Adoke na daga cikin waɗanda suka tsaya tsayin daka wajen shawartar Shugaba Jonathan ya amince da shan kaye bayan zaɓen 2015.

Tsohon gwamnan ya yi mamakin yadda daga baya ya fuskanci matsin lamba daga gwamnatin da ta biyo baya.

Ya bayyana cewa zai karanta littafin domin samun cikakken haske kan lamarin.

“A zahiri, ya kamata mu gode masa a matsayinmu na gwamnati ta APC a shekarar 2015, ba wai a tsananta masa ba."

Kara karanta wannan

An hango Kashim Shettima, Kwankwaso, El-Rufa'i da Saraki tare a Abuja

"Na tattauna da Shugaba Buhari sau da dama, kamar yadda kuka sani ina kusa da shi sosai, kuma ban ga yana da wani buri na musamman a cikin wannan batu ba sai dai mutunta doka da oda."

- Nasir El-Rufai

Nasir El-Rufai ya yi magana kan littafin Adoke
El Rufai ya ba da shawara ga masu mukami Hoto: @elrufai
Source: Twitter

Batun OPL 245, wanda aka fi sani da badaƙalar Malabu, na da nasaba da yadda kamfanonin Shell da Eni suka mallaki lasisin hakar mai (OPL 245) a shekarar 2011 da kuɗi dala biliyan $1.3.

Asalin rigimar na da nasaba da zargin cewa, wani kaso mai yawa daga cikin kuɗin, musamman dala biliyan $1.1, an karkatar da su ta hannun wasu masu shiga tsakanin gwamnati don bai wa wasu jami’an gwamnati da ƴan siyasa cin hanci.

Adoke, wanda gwamnatin Muhammadu Buhari ta jawo cikin lamarin, daga bisani kotu ta sallame shi daga tuhuma a cikin gida da kuma waje.

El-Rufai ya yi magana kan ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi magana kan jam'iyyar haɗaka ta ADC.

El-Rufai ya bayyana cewa ƴan adawa za su iya yin fito na fito da jam'iyyar APC a babban zaɓe mai zuwa na shekarar 2027.

Kara karanta wannan

Kudirin ƙirƙiro karin jiha 1 a Arewacin Najeriya ya samu gagarumin goyon baya a Majalisa

Tsohon gwamnan ya bayyana cewa hakan ne ma dalilin da ya suka amince wajen yin amfani da ADC don ceto ƙasar nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng