'Yan Bindiga Sama da 400 Sun Kai Hari a Kebbi, an Yi Gumurzu da Dakarun Sojoji
- Dakarun sojojin Najeriya sun nuna bajinta a yayin artabun da suka yi da ƴan bindiga a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma
- Sojojin sun samu nasarar daƙile yunƙurin da ƴan bindigan suka yi na.ƙwace garin Ribah da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu
- Jami'an tsaron sun kuma samu nasarar hallaka ƴan bindiga da dama tare da ƙwato makamai masu tarin yawa a hannunsu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kebbi - Bataliya ta 223 ta rundunar sojojin Najeriya da ke Zuru a jihar Kebbi, ta samu nasarar daƙile wani gagarumin hari da ƴan bindiga suka kai.
Ƴan bindigan sun kai harin ne a garin Ribah, da ke ƙaramar hukumar Danko Wasagu ta jihar Kebbi.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce harin da ya faru a ranar Laraba ya haɗa da fiye da ƴan bindiga 400 da ke ɗauke da muggan makamai, waɗanda suka ƙuduri aniyar kwace garin Ribah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun daƙile harin ƴan bindiga
Sai dai sojoji sun mayar da martani, inda aka yi artabu mai tsanani da ƴan ta’addan, yayin da aka kashe da dama daga cikinsu a fafatawar.
Ko da yake wasu daga cikin ƴan bindigan sun samu nasarar kwashe gawarwakin abokansu da suka mutu, an bar wasu gawarwaki da kuma tarin makamai da dakarun suka ƙwato, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
Daraktan tsaro na ofishin majalisar zartarwar jihar, Alhaji AbdulRahman Zagga, ya tabbatar da aukuwar lamarin a Birnin Kebbi, inda ya yaba da jarumta da jajircewar sojojin Najeriya.
Ya ce duk da cewa adadin maharan ya kasance barazana a farko, ƙwarewar sojoji da ƙudurinsu ya taimaka wajen juya akalar lamarin zuwa nasara ga rundunar tsaro.
Sojoji sun samu yabo
Alhaji AbdulRahman Zagga ya kuma yaba da ɗaukin da rundunar sojojin sama ta kawo, inda jirgin yaƙinta ya riƙa luguden wuta kan ƴan bindigar da ke tserewa, wanda hakan ya yi sanadiyyar kashe da dama daga cikinsu.
“Ko da yake harbe-harben farko sun haifar da firgici da ruɗani a cikin al’umma, an riga an shawo kan lamarin, kuma komai ya koma daidai yadda ya kamata."
"Komai ya lafa yanzu. Mutanen Ribah za su iya numfasawa cikin natsuwa, saboda ƙoƙarin da jami’an tsaro suka nuna."
- Alhaji AbdulRahman Zagga

Source: Original
Ya ƙara da cewa ana zargin maharan su ne suka kai hari a jihar Neja kwanan nan.
"Sun ƙetaro zuwa Kebbi domin ƙaddamar da wani sabon hari, wanda aka dakile gaba ɗaya, abin da ya nuna tasirin matakan tsaro da aka ɗauka ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris."
- Alhaji Abdulrahman Zagga
Sojoji sun hallaka ƴan Boko Haram/ISWAP
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojoji na rundunar Operation Hadin Kai sun yi raga-raga da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP.
Sojojin sun hallaka ƴan ta'adda 24 a jerin hare-harrn da suka kai a maɓoyarsu da ke jihohin Borno da Adamawa.
Hakazalika sun ƙwato makamai masu tarin yawa tare da babura da kekuna waɗanda ƴan ta'addan suke amfani da su.
Asali: Legit.ng

