Tsaro: Nuhu Ribadu Ya ba Tinubu Kariya, Ya Gargadi 'Yan Adawan Najeriya

Tsaro: Nuhu Ribadu Ya ba Tinubu Kariya, Ya Gargadi 'Yan Adawan Najeriya

  • Mai bai wa shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu, ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu shugaba ne mai hangen nesa da kwazo
  • Malam Nuhu Ribadu ya ce wadanda ke sukar mulkin Tinubu tsofaffin ‘yan siyasa ne da suka kasa da gaza kawo ci gaba a baya
  • Ya ce Najeriya na samun tsaro da kwanciyar hankali a kullum saboda irin dabarun mulki da gwamnatin Tinubu ke amfani da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro na ƙasa, Mallam Nuhu Ribadu, ya gargadi ‘yan adawa da kada su raina ƙarfin shugabancin Bola Ahmed Tinubu.

Ribadu ya bayyana haka ne a wani taron tsaro da aka gudanar a birnin tarayya Abuja, inda ya ce gwamnati na samun nasara wajen kawo zaman lafiya da ci gaba a fadin ƙasar.

Kara karanta wannan

Bauchi: Sarakuna sun aika sako ga magoya baya kan shirin kirkirar sababbin masarautu

Nuhu Ribadu ya ce Tinubu na samun nasara a Najeriya
Ribadu ya ce Tinubu na samun nasara a Najeriya. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Vanguard ta rahoto ya ce Najeriya yanzu ta zama kasa mai jawo hankalin masu saka hannun jari, saboda manufofin tattalin arziki da tsarin tsaro na gwamnatin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Tsaro ya inganta karkashin Tinubu,' Ribadu

Nuhu Ribadu ya ce ana samun gagarumar nasara a yankunan da ke da rikici, musamman yankin Neja Delta da Kudu maso Gabas, inda ya ce Najeriya na kara samun kwanciyar hankali kullum.

Ya ce:

"Neja Delta yanzu lafiya lau. Kudu maso Gabas na dawowa daidai. Za a gano wadanda ke tada hankali daga kasashen waje, kuma za a hukunta su. Ba za mu bari a rusa cigaban da muke yi ba."

Martanin Ribadu kan sukar gwamnatin Tinubu

Ribadu ya ce yawancin wadanda ke sukar gwamnatin Tinubu tsofaffin ‘yan siyasa ne da suka lalata ƙasar a baya.

The Guardian ta rahoto Ribadu ya ce:

“Waɗannan mutane sun lalata ƙasar nan. A yau suna yawo suna sukar gwamnati a kafafen yaɗa labarai. Najeriya ta ci gaba – kuma ‘yan Najeriya sun waye.”

Kara karanta wannan

Ana maganar hadaka, Dangote ya rubutawa Bola Tinubu budaddiyar wasika

Ya ƙara da cewa Tinubu na kafa tubalin sabuwar Najeriya wadda ke da kwanciyar hankali da tattalin arziki mai ɗorewa, tare da jawo hankalin masu saka hannun jari daga kasashen waje.

'Tinubu shugaba ne na zamani' Ribadu

Ribadu ya bayyana Bola Tinubu a matsayin shugaba na zamani wanda ke amfani da fasaha da basira wajen jagorantar kasa.

A cewar shi:

“Muna da shugabanci mai inganci a yau. Shugaban kasa mutum ne mai ilimi da hangen nesa. Wanda ya raina shi yana yi wa kansa ne.”
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a ofis
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro a ofis. Hoto: Nuhu Ribadu
Source: Twitter

Ya kuma bukaci kamfanonin sadarwa, masu kirkire-kirkire a fasaha da ‘yan kasuwa daga kasashen waje da su saka jari a Najeriya, yana mai cewa kasar ta zama cibiyar tattalin Afrika.

Dangote ya yaba wa shugaba Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa Alhaji Aliko Dangote ya rubuta wa shugaba Bola Ahmed Tinubu budaddiyar wasika kan kokarin da ya yi a kan mulki.

Alhaji Aliko Dangote ya yaba da yadda Bola Tinubu ke ayyuka a Najeriya, musamman hanyoyi a yakuna daban daban na kasar.

Dangote ya yaba da yadda ake kokarin shawo kan ambaliyar ruwa tare da alkawarin tallafawa wadanda ambaliya ta shafa a Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng