Bayan Zargin Badakala, Peter Obi Ya Fadi Alakar da Ta Hada Shi da Abacha
- Peter Obi ya ce dangantakarsa da marigayi Janar Abacha ta samo asali ne daga kokarin gyara harkokin tashar jiragen ruwa
- Tsohon dan takarar shugaban kasa ya fitar da wata takarda da ke nuna yadda aka nada shi a kwamitin rage cunkoso a tashoshi
- Obi ya jaddada cewa bai taba haduwa da Abacha a baya ba sai dai a lokacin da matsalar kasuwanci ta tilasta musu hakan
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar LP, Peter Obi, ya fayyace dangantakarsa da marigayi shugaban kasa Janar Sani Abacha.
Peter Obi ya yi magana yana mai cewa alakarsu ta ta’allaka ne kacokan da kokarin inganta harkokin tashar jiragen ruwa, ba siyasa ba.

Source: Facebook
Obi ya bayyana haka ne a X yayin da yake martani kan zarge-zargen da suka taso a baya-bayan nan dangane da alakar da ake rade-radin yana da ita da Abacha.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce dole ne ya fito fili da hujjoji domin kare gaskiya da kuma bayyanawa al’umma cewa abin da ya faru a wancan lokaci aikin kishin kasa ne ba wata manufa ta siyasa ba.
Me ya hada Peter Obi da Sani Abacha?
Obi ya ce shi da wasu ‘yan kasuwa sun tuntubi gwamnati a lokacin Abacha ne saboda dogon jinkiri wajen fitar da kaya daga tashar ruwa wanda ke shafar harkokin kasuwanci da tattali.
Jaridar Punch ta wallafa cewa Peter Obi ya ce:
“Mun je wajensa ba a matsayin ‘yan siyasa ba, sai a dai matsayin ‘yan kasuwa da ke neman mafita kan matsalar da ke janyo cikas ga kasuwancin al’umma.”
Obi ya bayyana cewa wannan yunkuri ya haifar da kafa kwamitin da zai rage cunkoso a tashar ruwa, kuma daga nan ne aka nadashi a matsayin daya daga cikin mambobin kwamitin.

Source: Getty Images
Abacha: Obi ya fitar da hujja don kare kansa

Kara karanta wannan
An tsinci gawar ministan sufuri awanni bayan shugaban kasa ya kore shi daga aiki a Rasha
Domin kara tabbatar da ikirarin nasa, Obi ya wallafa wata wasika da ke nuna cewa an nada shi a matsayin mamba na kwamitin aikin rage cinkoso a tashoshin jiragen ruwa a zamanin Abacha.
Peter Obi ya ce:
“Wannan bayani na da muhimmanci ne don tabbatar da gaskiya, domin mutane su fahimci cewa aikina a lokacin ya ta’allaka ne da kishin kasa ba siyasa ba.”
Obi ya kara da cewa yana sane da cewa akwai masu neman bata masa suna, amma ya ce fitar da gaskiya a fili na daga cikin alkawuran da ya dauka ga ‘yan Najeriya.
Ya kara da cewa:
“Ko da kuwa ba za su yarda ba, an fitar da gaskiyar ne a fili domin kiyaye tarihi da kuma kara nuna gaskiyata a duk abin da nake ciki.”
2027: Peter Obi ya yi wa Arewa alkawari
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya yi magana game da Arewa.
Peter Obi ya bayyana cewa idan har ya samu nasara a zaben 2027, 'yan Arewa za su ji dadin mulkin da zai yi.
Obi ya bayyana haka ne yayin da ya ke jaddada cewa zai tsaya takara a zaben 2027 ana tsaka da maganar hadakar 'yan adawa.
Asali: Legit.ng
