UAE Ta Ƙaƙaba Takunkumi game da Shiga Kasarta ga Wasu Rukunin 'Yan Najeriya
- Hukumomin shige da fice na Dubai sun sanar da cewa ba za a ƙara karɓar buƙatun biza ta wucewa ta kasarta daga Najeriya ba
- Wannan sabon mataki na zuwa ne bayan gwamnatin kasar nan ta shawo kan hukumomin Dubai da kyar a kan matsalar biza
- Daga cikin wadanda lamarin ya fi shafa akwai yan shekaru 18 zuwa 45 da ke son zuwa Hadaddiyar Daular Larabawa yawon bude ido
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
United Arabs Emirate – Hukumomin Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) sun ƙara tsaurara sharuddan samun biza ga 'yan Najeriya.
Wannan ya shafi yan kasar nan da ke son shiga birnin Dubai, tare da haramta daukar sababbin tsarin biza ga masu yawon bude ido.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sabon umarnin ya iske wakilan masu tafiye-tafiye a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dubai ta sanya wa yan Najeriya takunkumi
Jaridar Tribune Online ta wallafa cewa ana ganin wannan sabon mataki na UAE a matsayin babban sauyi da za a iya amfani da shi wajen rage cunkoson 'yan Najeriya da ke shiga Dubai.
Hukumomin UAE sun sanya matakan, musamman ga 'yan Najeriya masu shekaru tsakanin 18 zuwa 45.
Sababbin tsare-tsaren sun ce wadanda ke tsakanin wadannan shekaru ba za su iya samun biza ta yawon buɗe ido ba sai idan suna tare da abokin tafiya.

Source: Facebook
Wannan na zuwa ne kusan shekara guda bayan Najeriya da UAE sun warware matsalar haramcin biza da aka sanya wa 'yan Najeriya tsawon shekara biyu.
Sai dai duk da cewa an ɗage takunkumin, UAE ta ci gaba da sanya wasu sharudda masu tsauri da suka rage yawan 'yan Najeriya da ke iya shiga ƙasar.
Sababbin dokokin Dubai ga 'yan Najeriya
Rahotanni sun ce sababbin umarnin da Ofishin Shige da Fice na Dubai ya isa ga wakilan yawon shakatawa a ranar Talata.
Daga cikin sharuddan akwai:
“Ba za a ƙara karɓar buƙatun biza ta wucewa ta kasar wato 'transit visa' daga Najeriya ba.”
Sannan sanarwar ta ƙara da cewa:
“Ga ɗan Najeriya, wanda shekarunsa ke tsakanin 18 zuwa 45 kuma yana tafiya shi kaɗai ba ya cikin waɗanda za su iya samun biza ta yawon buɗe ido.”
“Duk mai shekaru 45 ko fiye dole ne ya gabatar da bayanan asusun bankinsa na tsawon watanni shida da suka gabata, tare da nuna cewa a ƙarshen kowanne wata, asusun na da adadin kudi mafi ƙaranci na dala $10,000 ko daidai da hakan a Naira).”
Ana bayar da bizar shiga UAE
A baya, mun kawo maku labarin cewa an gano cewa hukumomin UAE ta dage takunkumin da ta sanya na hana ‘yan Najeriya samun biza.
Tun a watan Oktoban 2022, gwamnatin Hadaddiyar Daular Larabawa ta haramta ba wa ‘yan wasu ƙasashen Afrika 20 biza, ciki har da Najeriya.
Wannan takunkumi ya sa dangantaka tsakanin Najeriya da UAE ta shiga wani hali, musamman kan batun jiragen sama da izinin shige da fice kasashen.
Asali: Legit.ng


