Aminu Ado Bayero Ya Yi Magana, Ya Faɗi Abin da Magoya Bayansa Suka Yi a Fadar Sanusi II
- Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya musanta zargin da ake cewa magoya bayansa ne suka fara tayar da rikici a Fadar Ƙofar Kudu ranar Lahadi
- Basaraken ya bayyana cewa babu wanda ke ɗauke da makami daga cikin magoya bayansa a lokacin da ya zo wucewa ta fadar bayan dawowa daga ta'aziyya
- Aminu Bayero ya ce wasu matasa ne suka farmaki ayarinsa da duwatsu, lamarin da ya tilasta masu ƙoƙarin kare kansu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero ya ce ba da gangan magoya bayansa suka shiga rigima a Fadar Kofar Kudu da Muhammadu Sanusi II ke zaune ba.
Aminu Ado, wanda gwamnatin Kano ta tube daga sarauta, ya ce magoya bayansa sun yi kokarin kare kansu ne a lokacin da aka tare su da faɗa ranar Lahadi.

Source: Facebook
Leadership ta rahoto cewa rikici ya auku tsakanin masoyan Aminu da masoyan Sanusi II a Fadar Sarkin Kano da Ƙofar Kudu ranar Lahadi da ta gabata.
Gwamnatin jihar Kano ta bayyana wannan hatsaniya a matsayin abin takaici, inda ta ce wasu fararen hula da babu ruwansu sun samu raunuka.
Masarautar Kano ta ɗora laifi kan Aminu Ado
A wata sanarwa da masarautar Kano ta fitar ɗauke da sa hannun Sadam Yakasai, ta ce Mai Martaba Muhammasu Sanusi II ba ya nan lokacin da aka farmaki fadarsa.
A rahoton Daily Post, sanarwar ta ce:
"Sun fasa ƙofar gidan suka kai wa masu gadi hari, inda wasu daga cikinsu suka jikkata. Sun lalata motar ‘yan sanda da ke cikin fadar.
"Aminu Bayero ya wuce ta hanyar gidan Sarki da gangan maimakon ya bi hanyar da ta dace daga Koki zuwa Nassarawa, sannan 'yan daba da ke tare da shi suka kai hari gidan Rumfa."

Kara karanta wannan
Harin da aka kai Fadar Sarki Muhammdu Sanusi II ya ƙara tayar da ƙura a jihar Kano
Aminu Ado Bayero ya musanta tayar da rikici
Sai dai a martaninsa kan abin da ya faru, Sarki Aminu Ado Bayero ya musanta zargin kai hari Fadar Sanusi II, yana mai cewa magoya bayansa sun yi ƙoƙarin kare kansu ne.
Mai taimaka wa Sarki Bayero kan harkokin yaɗa labarai, Khalid Uba, ya shaida wa manema labarai cewa babu makamai a hannun magoya bayan Aminu Ado.
Khalid Uba, wanda ya yi magana da wakilin jaridar ta wayar salula, ya jaddada cewa babu wanda ke cikin tawagar Sarki Bayero da ke ɗauke da makami.

Source: Twitter
Me magoya bayan Aminu suka yi a fadar Sanusi?
Amma a cewarsa, ƴan daban da ke Fadar Sarki Sanusi ne suka fara kai masu hari, wanda hakan ya tilasta musu su ƙoƙarin kare kansu daga harin.
“Wannan ba shi ne karo na farko da Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ke bi ta wannan hanya ba. Mun dawo daga ta'aziyya gidan Ɗantata, muka haɗu da wasu matasa ɗauke da duwatsu da makamai sun toshe hanya.
“Da muka karaso kusa da Kofar Kudu, sai suka fara jifar mu da duwatsu amma bisa sa'a muka ci galaba muka kore su, Sarki ya wuce lami lafiya ba tare da kowa ya ji rauni ba.
- Khalid Uba.
Yan sanda sun fara bincike kan rikicin Ƙofar Kudu
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sanda ta jihar Kano ta kafa wani kwamitin bincike don gano abin da ya jawo hatsaniyar da ta faru a Fadar Sarkin Kano.
Mai magana da yawun ƴan sandan Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar rikici tsakanin magoya bayan sarakunan Kano biyu.
Ya ce kwamishininan ƴan sandan Kano ya kafa kwamitin da zai binciko ainihin abin da ya faru domin ɗaukar matakin da ya dace.
Asali: Legit.ng

