‘Ba Mu Taɓa Zagin Sarki ba’: Masoyan Aminu Ado da Aka Kora a Fada Sun Yi Martani
- Daya daga cikin wadanda aka wulakanta a fadar Sarki Sanusi II ya ce har abada ba za su bar soyayya ga Aminu Ado Bayero ba
- Usman Sallama Dako ya koka kan yadda iyalansu ke fuskantar tozarci da rusau a gidan, yana zargin Sarki Sanusi da rashin adalci da tausayi
- Dako ya bayyana cewa shi bawan gidan masarauta ne, kuma zai cigaba da biyayya da kauna ga Aminu Ado duk da kaddarar rayuwa.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Yayin da ake cigaba da rigima bayan korar wasu masoyan Aminu Ado daga fadar Muhammadu Sanusi II, lamarin ya sake daukar zafi.
Daya daga cikinsu, Alhaji Usman Sallama Dako wanda yana daga cikin bayi da abin ya shafa ya tura sako ga Sarki Sanusi II.

Source: Twitter
Martanin bayi bayan korarsu a fadar Sanusi II
Hakan na cikin wani faifan bidiyo da shafin Masarautar Kano ta wallafa a Facebook a yammacin yau Talata.
Dako ya ce a matsayinsa na bawa ya yi mamakin abin da yafu inda ya tunawa yan sarauta yadda zamansu take tun a baya.
Sallama Dako ya ce su kam har su mutu ba za su bar kaunar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ba saboda shi ne ya mayar da su mutane.
Ya ce:
"Ni bawan Sarki ne ba na wuce kaddara ta da bautar Sarki, amma su da suke ganin sune manyanmu kamar Shamaki, Sallama da Dan Rimi ba su da tarihin kiyayyar bawan sarki da sarki?.
"Mun taba zagin Sarki Sanusi ne idan zai wuce a kan hanya?, idan dai Sarki ne kuma ya yarda shi Sarki ne su kuma sun yarda bayin Sarki ne ya kamata su san wannan tarihi.
"Kaddarar Allah ce kaso mutum a cikin ranka, har Sarkin Kano, Ado ya rasu akwai wadanda ba su zuwa su gaishe shi, meye ya musu?"

Kara karanta wannan
Rikicin sarauta: Gwamnatin Kano ta fito ta fayyace abin da ya faru a Fadar Sanusi II
"Ina ruwansa ma da su, sai mu za a yiwa tozarci da iyalanmu a gida ana daye mana kwano ana rusa mana garu."
Sallama ya koka kan irin tozarci da aka yi musu a fadar Sarki Sanusi II duk da cewa a gidan aka haifi har mahaifansu.
Ya jaddada cewa har su mutu ba za su bar kaunar Aminu Ado ba saboda gatan da suka yi musu suka mayar da su mutane.
Ya kara da cewa:
Shi yana da'awar malami ne shi zai hau kan mimbari ya yi huduba bai san menene hakkin mutum ba, ko kafiri ba za ka yiwa haka ba.
"Cibiyar mahaifi na a gidan take, ni ma a nan aka haifen, ba ni da gadon gidan ne?, bawan gidan ne ni ina da gadon gidan.
"Wanda muke tare da shi sai dai su yanka mu a kansa, ba za mu fasa binsa ba, ba za mu fasa soyayyarsa ba, mun yarda iyayensa sun mayar da mu mutane."
An kori masoyan Aminu Ado a fadar Sanusi
Kun ji cewa Masu biyayya ga Aminu Ado Bayero sun fuskanci matsala daga fada, saboda rashin goyon bayan Sarki Muhammadu Sanusi II.

Kara karanta wannan
Sanusi II ya yi magana kan rigimar da ta faru a fadarsa da Aminu Ado ya zo wucewa
Wasu jami’an fada da iyalansu sun sha ruwan ihu yayin da aka zargi ’yan daba da balle rufin gidajensu domin tilasta musu fita.
Hakan ya biyo bayan zarginsu da goyon bayan Aminu Ado yayin da suke fadar Sarki Sanusi II.
Asali: Legit.ng
