Momodu Ya Yi wa Wike Tonon Silili bayan Sukar Masu Hadaka a ADC

Momodu Ya Yi wa Wike Tonon Silili bayan Sukar Masu Hadaka a ADC

  • Fitaccen dan jarida Dele Momodu ya zargi Ministan Abuja, Nyesom Wike da 'bautar' mulki da kudi wajen cutar da abokansa na baya
  • Dele Momodu ya bayyana cewa Nyesom Wike ya ci gajiyar kamfaninsa na Ovation wajen gyara shi yadda zai shiga jama’a da kyau
  • Ya ce girman kai da son mulki sun lalata Wike, kuma yana amfani da karfi da kudi wajen take hakkin mutane a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Dan jarida kuma dan siyasa, Dele Momodu, ya yi wa Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, wankin babban bargo.

Dele Momodu ya zargi Nyesom Wike da cutar da abokan tafiyarsa na baya domin cimma muradun karan kansa.

Momodu ya zargi Wike da juya wa mutanen da suka taimake shi baya
Momodu ya zargi Wike da juya wa mutanen da suka taimake shi baya. Hoto: Dele Momodu|Nyesom Ezonwo Wike
Source: Twitter

Momodu ya yi wannan magana ne a wata hira mai zafi da aka yi da shi a Channels TV, inda ya bayyana yadda dangantakarsa da Wike ta lalace.

Kara karanta wannan

Makircin Bello Turji na neman shirya sulhu da gwamnati ya fito fili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, Wike mutum ne da ke girmama jama'a idan yana bukatar su, amma idan bukatarsa ta biya, sai ya yi watsi da su.

Momodu ya ce ya yi wa Wike gata

Momodu ya bayyana cewa kamfaninsa na Ovation ne ya tallafa wa Wike wajen inganta yadda zai saka tufafi da koya masa yadda zai yi magana a idon jama’a.

Jaridar Guardian ta wallafa cewa Dele Momodu ya ce:

“Mun shirya shi tsaf kan yadda zai rika saka sutura, mun koya masa yadda zai yi magana da kwarjini a idon duniya,”

Momodu ya kara da cewa Wike ya ci gajiyar baiwar da Allah ya ba shi, amma daga baya ya juya masa baya tare da nuna masa isa da girman kai.

Momodu na wata ganawa da Bola Tinubu.
Momodu na wata ganawa da Bola Tinubu. Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Momodu ya ce Wike mayen kudi ne

Dele Momodu ya ce Wike ya koma aikata irin abin da yake korafi a kai a baya, inda ya kwatanta shi da irin wadanda suka zalunce shi a baya.

Kara karanta wannan

Allah sarki: Yan bindiga sun kai hari, sun hallaka basarake da wasu mutum 2

A cewar Momodu:

“Wike mutum ne da ke girmama masu mulki da madafun iko, amma idan ya samu dama, sai ya fi su zalunci,”

Ya kuma bayyana cewa Wike na da matsala da shan giya, inda ya ce:

“Ya taba ce min giya mai karfi ‘Akeshi’ tana taimaka masa aiki da safe.”

Alakar rikicin Wike da Momodu da 2027

Wannan rikici na siyasa na faruwa ne a daidai lokacin da ake shirin babban zaben 2027, inda dangantakar siyasa ke sauyawa a Najeriya.

Dele Momodu da Wike, wadanda suka taba kasancewa abokan siyasa, yanzu sun koma gaba da juna, lamarin da ke kara zafafa siyasar adawa.

Ana ganin hakan na da alaka da yadda Wike ke nuna goyon baya ga Bola Tinubu yayin da Momodu ke goyon bayan Atiku Abubakar.

ADC ta zargi Tinubu da mata makarkashiya

A wani rahoton, kun ji cewa jam'iyyar adawa ta ADC ta zargi gwamnatin Bola Tinubu da shirya mata makarkashiya.

Kara karanta wannan

An kai Wike bango, ya ce zai yi murabus daga matsayin Ministan Abuja bisa sharaɗi 1

Hakan na zuwa ne yayin da lamuran siyasa ke kara daukar zafi a Najeriya gabanin zaben shekarar 2027.

ADC ta ce gwamnatin Bola Tinubu ta fara shirya taron sirri da tsofaffin shugabannin ADC a jihohi domin dagula jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng