Bayan Jita Jitar Zai Bar APC, Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Nasarawa Muƙami

Bayan Jita Jitar Zai Bar APC, Tinubu Ya Naɗa Tsohon Gwamnan Nasarawa Muƙami

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada tsohon gwamnan Nasarawa a mukami a hukumar UBEC a Najeriya
  • Ministan ilimi Tunji Alausa ne ya jagoranci rantsar da shi yayin wani taro da ya shafi cigaban fasaha a jami’o’i a Abuja
  • Tanko Al-Makura zai jagoranci tsara manufofi da dabarun da za su bunkasa ilimi, tare da hadin gwiwa da gwamnoni da kananan hukumomi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada tsohon gwamnan Nasarawa muƙami a gwamnatinsa.

Tinubu ya ba Tanko Umaru Al-Makura muƙamin shugaban majalisar sa ido a hukumar ilimi na bai ɗaya da ake kira UBEC.

Tinubu ya ba Al-Makura muƙami a gwamnatinsa
Tinubu nada tsohon gwamnan Nasarawa muƙami. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Ministan ilimi a Najeriya, Tunji Alausa shi ne ya jagoranci rantsar da shi ranar Talata yayin kaddamar da wani shirin bunkasa harkokin sadarwa a jami’o’i a Abuja, cewar TheCable.

Kara karanta wannan

2027: Atiku, Sule Lamido da jiga jigan PDP sun shiga ganawar gaggawa a Abuja

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hasashen shugabancin APC da ake yiwa Al-Makura

Al-Makura yana daya daga cikin wadanda ake ta hasashen zai iya zama shugaban APC mai mulkin Najeriya.

Hakan ya biyo bayan murabus din tsohon shugaban jam'iyyar, Dr. Abdullahi Umar Ganduje a ranar Juma'a da ta gabata.

Tsohon gwamnan Nasarawa wanda ya fito daga Arewa ta Tsakiya da ke daga cikin yankunan da ake sa ran sabon shugaban jam'iyyar zai fito.

Muƙaman da Sanata Al-Makura ya rike a baya

Tanko Umaru Al-Makura dan kasuwa ne kuma ɗan siyasa, ya yi mulki sau biyu a Nasarawa daga 2011 zuwa 2019 karkashin jam’iyyar CPC.

Al-Makura ne kadai gwamna a karkashin CPC da aka zaba a zaben 2011 a fadin kasar nan a wancan lokaci.

Bayan ya kammala gwamnatinsa, ya wakilci yankin Nasarawa ta Kudu a majalisar dattawa daga 2019 zuwa 2023.

Al-Makura yana da kwarewa a harkar injinan noma da masana’antu, kadarori, da kuma otal-otal.

Kara karanta wannan

"Ba dan Allah ba ne," An gano abin da ke tilastawa gwamnonin PDP sauya sheƙa zuwa APC

Tinubu ya gwangwaje Al-Makura da muƙami a gwamnatinsa
Tinubu ya ba tsohon gwamnan Nasarawa, Al-Makura mukami. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

Abin da ake tsammani daga Al-Makura a hukumar

A matsayin shugaba a hukumar, ana sa ran zai jagoranci tsara manufofi da hanyoyin tafiyar da shirin ilimin firamare.

Zai rika aiki da shugabannin hukumar wajen tsara dokoki don tabbatar da nasarar aiwatar da tsarin UBEC, Daily Post ta ruwaito.

Ayyukansa sun hada da ba gwamnati shawara kan kudade da ci gaban shirin, da kuma hada kai da jihohi da kananan hukumomi.

Haka kuma zai dora kan kafa mafi karancin mizani na ingancin ilimi a matakin firamare a fadin kasar baki daya domin kawo sauyi a bangaren ilimi a kasar.

Al-Makura ya maye gurbin Idris Olorunnimbe wanda aka nada shugaban sa ido a hukumar UBEC a watan Maris ta shekarar 2025.

Tinubu ya ba tsohon kakakin majalisa, Dogara muƙami

Kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kafa kamfanin ba da lamuni na kasa (NCGC), inda Yakubu Dogara ya zama shugaban kwamitin gudanarwa.

Kara karanta wannan

Ganduje: Jerin shugabannin APC da yadda suka sauka daga shugabanci

NCGC zai rage hadarin bayar da bashi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, matasa, mata da masana’antu don inganta tattali.

Kamfanin zai fara aiki a watan Yulin 2025, tare da goyon bayan Bankin Duniya da hukumomin MOFI, NSIA, BOI da CrediCorp domin inganta kasuwanci da tattalin arziki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.