Bola Tinubu Ya Yi Zarra a Kasar St. Lucia, an ba Shi Lambar Yabo Mafi Girma

Bola Tinubu Ya Yi Zarra a Kasar St. Lucia, an ba Shi Lambar Yabo Mafi Girma

  • Gwamnatin Saint Lucia ta bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu lambar girmamawa mafi girma ta COSL a kasar Saint Lucia
  • Bola Tinubu ya ce ziyarsa na nufin ƙarfafa dangantaka tsakanin Afirka da yankin Caribbean ta fuskar tattalin arziki da al’adu
  • Rahoto ya nuna cewa ana shirin ƙarfafa alaƙar diflomasiyya tsakanin Najeriya da Saint Lucia ta hanyar shirin hadin gwiwa da agaji

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin ƙasar Saint Lucia ta karrama shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, da lambar girmamawa mafi daraja a ƙasar ta KCOSL.

An karrama shugaban kasar ne yayin da ya ke rangadin diflomasiyya a yankin Caribbean da Kudancin Amurka.

An ba Bola Tinubu lambar yabo a kasar Lucia
An ba Bola Tinubu lambar yabo a kasar Lucia. Hoto: Dada Olusegun
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan yadda aka karrama shugaba Bola Tinubu ne a cikin wani sako da Dada Olusegun ya wallafa a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sake ɗauko mutumin Buhari, ya ba shi babban muƙami a gwamnatinsa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu, wanda ya isa Saint Lucia ranar Asabar, ya halarci zaman haɗin gwiwar majalisar dattawa da ta wakilai na ƙasar, inda ya yi jawabi kan haɗin kai tsakanin Afirka da yankin Caribbean.

Girmamawar da aka yi wa Tinubu a Saint Lucia

Lambar KCOSL da Tinubu ya samu na daga cikin mafi girma da ake bai wa fitattun shugabanni da suka bada gudunmawa wajen inganta dangantakar ƙasashe.

A jawabinsa, Tinubu ya ce:

“Ziyara ta a Saint Lucia na nufin samar da haɗin kai tsakanin Afirka da Caribbean. Muna son ƙarfafa dangantaka ta tattalin arziki da ilimi da kuma musayar al’adu.”

Shugaban ya ƙara da cewa Najeriya da Saint Lucia suna da tarihi da al’adu da manufa iri ɗaya, wanda ya sa gwamnatin sa ke da burin ƙarfafa hulɗar diflomasiyya da cinikayya tsakaninsu.

Najeriya da St Lucia za su ƙulla hulɗar diflomasiyya

A wani mataki na karfafa haɗin gwiwa, gwamnatin Saint Lucia ta bayyana cewa za ta fara hulɗar diflomasiyya da Najeriya domin samar da tsarin aiki mai inganci.

Kara karanta wannan

'Za ka dawo kan mulkin Rivers: Tinubu ya gindaya sharuɗa 3 masu tsauri ga Fubara

The Cable ta wallafa cewa gwamnatin kasar ta ce:

“Za a kafa tsarin saukaka biza ga masu fasfo ɗin diflomasiyya da na hukumomi daga kasashen OECS, tare da samun tallafi daga Najeriya.”

Har ila yau, Najeriya za ta ba da guraben karatu ga ‘yan ƙasashen mambobin OECS da kuma faɗaɗa ayyukan TAC a cikin ƙasashen yankin.

Tinubu ya hadu da dalibin Najeriya a Lucia
Tinubu na gaisawa da dalibin Najeriya a kasar Lucia. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Twitter

Jawabin Tinubu a Majalisar Saint Lucia

A jawabin sa a majalisar Saint Lucia, Tinubu ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa domin ci gaban al’umma baki ɗaya.

Shugaban ya ce:

“Muna da burin samar da cigaba, ƙaruwar arziki da kuma ƙarfafa zumunci tsakanin jama’ar Najeriya da na yankin Caribbean.”

Ziyarar Tinubu na zuwa ne a wani lokaci da Najeriya ke ƙoƙarin faɗaɗa tasirinta a matakin duniya ta hanyar diflomasiyya, fasaha da ilimi.

An bukaci Tinubu ya sa dokar ta baci a Arewa

A wani rahoton, kun ji cewa kungiyar dattawan Arewa ta NEF ta yi kira ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kan matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro, yakin Iran da Isra'ila

Kungiyar dattawan ta bukaci shugaba Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a Arewa domin shawo kan matsalolin yankin.

Hakan na zuwa ne yayin da matsalar tsaro da ta hada da garkuwa da mutane da Boko Haram cigaba da addabar mutanen Arewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng