An Kashe Jagoran 'Yan Banga, Saleh Fiya Fiya a Dajin Kaduna

An Kashe Jagoran 'Yan Banga, Saleh Fiya Fiya a Dajin Kaduna

  • An kashe kwamandan rundunar KADVIS a karamar hukumar Kubau, Saleh Shuaibu, wanda aka fi sani da Saleh Fiya-Fiya
  • Lamarin ya faru ne a cikin filin kiwo na Yardoka yayin da jami’an gwamnati suka kai ziyara domin aiwatar da wani umarni da aka ba su
  • Rahoto ya nuna cewa makiyayan da ke zama a filin kiwon sun yi bore kan shirin bai wa wani kamfani filin don zuba jari

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Wasu makiyaya da ke zaune a cikin filin kiwo na Yardoka da ke Kubau a Kaduna sun kashe shugaban hukumar tsaron KADVIS, Saleh Shuaibu da aka fi sani da Saleh Fiya-Fiya.

Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi yayin da jami’an gwamnati suka kai ziyara zuwa filin kiwon domin aiwatar da wani umarnin gwamnati da ya shafi mallakar filin ga wani kamfani.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban Fulani a Kogi, sun harbi iyalan shi da AK47

An kashe dan banga Fiya Fiya a Kaduna
An kashe dan banga Fiya Fiya a Kaduna. Zagazola Makama
Source: Facebook

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa Saleh Fiya-Fiya ya yi yunkurin sasanta mutanen da suke samu sabani, amma daya daga cikinsu ya sare shi da wuka.

Yadda aka fara rikici a dajin Kaduna

Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an gwamnatin jihar Kaduna sun isa filin tare da ‘yan sanda da jami’an DSS domin aiwatar da tsarin mallakar sama da hekta 200 na fili ga wani kamfani.

Sai dai, al’ummar da ke zaune a yankin sun hana jami’an shiga, inda suka ce ba a biya su diyya ba, yayin da wasu ke cewa an riga an biya su amma har yanzu suna neman ƙarin kuɗi.

Taron ya rikide zuwa rikici, inda masu bore suka taru da takubba da sanduna suka hana jami’an tsaro da na gwamnati shiga filin.

Yadda aka kashe Saleh Fiya Fiya a Kaduna

A cewar wata majiya daga Anchau, hedkwatar gundumar Kubau, Saleh Shuaibu ya fito daga motar jami’an tsaro da nufin sasanta tsakanin jami’an gwamnati da masu zanga-zanga.

Kara karanta wannan

An harbe dan bindiga, Mai Jakka da yake wa 'yan Najeriya barazana a TikTok

A yayin da yake kokarin tattaunawa da su, wani daga cikin masu zanga-zangar ya sare shi da wuka, inda nan take ya riga mu gidan gaskiya.

Rahoton bai bayyana ko an kama wanda ake zargi da aikata kisan ba, sai dai an ce lamarin ya tayar da hankula a yankin.

Zargin rashin adalci a rabon fili a Kaduna

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa gwamnatin jihar na yunkurin karɓe ƙasar ne ba tare da bin ka’ida ba, suna korafi kan rashin adalci da rashin jin ƙorafinsu.

Sai dai wasu na cikin al’ummar sun ce gwamnati ta riga ta biya wasu daga cikin mazauna Yardoka diyya, amma ana ci gaba da neman ƙarin kudi da ƙorafi a kan lamarin.

A halin yanzu dai, an kara tura jami’an tsaro yankin domin kwantar da tarzoma da tabbatar da doka da oda.

Gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba game da kashe Fiya Fiya
Gwamnatin Kaduna ba ta ce komai ba game da kashe Fiya Fiya. Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Ana cigaba da bincike kan kisan Fiya Fiya

Har yanzu hukumomin jihar Kaduna ba su fitar da wata sanarwa ba a hukumance kan kisan Saleh Fiya-Fiya.

Sai dai an bayyana cewa hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da bincike domin gano gaskiyar lamarin.

Kara karanta wannan

Za a kafa dokar kisa ga masu taimakon 'yan bindiga a Kebbi

An sace shugaban Fulani a Kogi

A wani rahoton, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai hari wani sansanin Fulani.

A yayin harin, maharan sun sace wani shugaban Fulani bayan jikkata matar shi da dan shi da suka kai masa dauki.

Rahoton da Legit Hausa ta samu ya nuna cewa an samu harsashin bindiga AK47 da dama a wajen bayan tafiyar 'yan bindigar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng