'Dan Shekara 24 Ya Yi Garkuwa da Abokinsa, Ya Karɓi Naira Miliyan 5.3 Kuɗin Fansa

'Dan Shekara 24 Ya Yi Garkuwa da Abokinsa, Ya Karɓi Naira Miliyan 5.3 Kuɗin Fansa

  • Rundunar 'yan sanda ta kama Muanaenye Chekwube Victor mai shekaru 24, bisa zargin sace abokinsa tare da karɓar N5.3m
  • Wanda ake zargin ya amsa laifinsa kuma yana ba 'yan sanda haɗin kai don kama sauran abokan aikinsa; za a kai shi gaban kotu
  • A wani lamarin na daban, 'yan bindiga sun sace Attahiru Ibrahim a Bature Daji, jihar Neja, bayan sun kasa sace wani ɗan sa kai

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Anambra - Rundunar 'yan sandan jihar Anambra ta kama wani matashi dan shekaru 24, mai suna Muanaenye Chekwube Victor, bisa zargin garkuwa da mutane.

Rundunar ta ce 'yan sanda da ke hedikwatar rundunar ta Uli sun kama Chekwube Victor a ranar 26 ga Yuni, 2025, bisa zargin sace abokinsa.

'Yan sanda sun kama dan shekaru 24 ya yi garkuwa da abokinsa a Anambra
Babban sufetan rundunar 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Dan shekara 24 ya yi garkuwa da abokinsa

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace shugaban Fulani a Kogi, sun harbi iyalan shi da AK47

Kakakin 'yan sandan Anambra, SP Tochukwu Ikenga, ya shaida cewa Victor tare da 'yan tawagarsa, sun karɓi N5.3m matsayin kudin fansa kafin sakin wanda suka sace, inji rahoton Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar SP Tochukwu Ikenga ta ce:

"'Yan sanda da ke hedikwatar 'yan sanda ta Uli da yammacin ranar 26 ga Yuni, 2025, sun gano tare da kama wani Muanaenye Chekwube Victor, dan shekaru 24, a kan wani rahoto na garkuwa da mutane."
"Binciken da ake yi ya nuna cewa wanda ake zargin ya hada baki da 'yan tawagarsa inda suka yi garkuwa da abokinsa tare da karɓar kuɗin fansa a kudin dalar Amurka daidai da N5.3m kafin suka saki wanda suka sace.
"Wanda ake zargin, yayin bincike, ya amsa cewa ya shirya garkuwar ta hanyar yaudarar abokinsa don ya raka shi ya ga wani abokin nasa."

Za a gurfanar da matashin gaban kotu

Bayan kama Chekwube Victor da kuma nadar bayanansa, rundunar ta bayyana cewa tana ci gaba da ƙoƙarin kama sauran 'yan tawagar tasa.

A halin yanzu, yana ba 'yan sanda haɗin kai ta hanyar bayar da bayanai don kama sauran 'yan tawagarsa, kuma zai fuskanci shari'a bayan an kammala bincike.

Kara karanta wannan

"Yadda aka wawure N1.09bn daga asusun gwamnatin Kogi a cikin kwanaki 3 kacal"

Sanarwar ta ƙara da cewa:

"Rundunar 'yan sanda za ta ci gaba da jajircewa wajen inganta tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma a jihar Anambra."
'Yan bindiga sun sace wani mutumi a kauyen Bature Daji da ke jihar Neja
Jami'an rundunar 'yan sanda da ke yaki da masu aikata miyagun laifuffuka. Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

'Yan bindiga sun sace mazaunin Bature Daji

Wannan ya zo ne a daidai lokacin da 'yan bindiga masu yawa suka mamaye garin Bature Daji a jihar Neja da sanyin safiyar Asabar, inda suka sace wani mazaunin garin.

Zagazola Makama ya rahoto cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 5:30 na safe lokacin da maharan suka mamaye gidan Dani, wani sanannen ɗan sa kai a yankin.

An ruwaito cewa 'yan bindigar sun kai harin ne musamman kan Dani, amma Allah ya ba shi nasarar tserewa.

Sai dai, 'yan bindigar sun sace wani Attahiru Ibrahim, wanda aka fi sani da Sarki Daji, a unguwar da shi Dani yake.

Saurayi ya jagoranci garkuwa da budurwarsa

A wani labarin, mun ruwaito cewa, 'yan sanda sun kama wani Ahmed bisa laifin hada kai da Uchenna Daniels wurin yin garkuwa da budurwarsa, Hannatu Kabri.

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali a Katsina, ƴan bindiga sun 'ƙwace ikon' karamar hukuma

An yi garkuwa da Kabri ne a Abuja, ranar 31 ga watan Maris inda aka zarce da ita jihar Legas, kuma an sako ta ne bayan iyayenta sun tura N2m a matsayin kudin fansa.

Bayan kai wa ‘yan sanda rahoto ne suka fara bincike don gano wanda ya yi aika-aikar daga nan suka kamo Uchenna Daniels wanda ya tona asirin Ahmed.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com