Ana Tsaka da Maganar Ganduje, an Yaɗa Murabus Ɗin Sakataren Gwamnati, Gaskiya Ta Fito

Ana Tsaka da Maganar Ganduje, an Yaɗa Murabus Ɗin Sakataren Gwamnati, Gaskiya Ta Fito

  • Fadar shugaban kasa ta yi magana kan jita-jitar cewa an sauya Sanata George Akume daga mukaminsa na sakataren gwamnatin tarayya
  • Mai ba shugaban kasa shawara kan bayanai, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa "babu wani sauyi" game da matsayin Akume, kuma ya ce Bola Tinubu bai nada wani ba
  • Fadar ta ce masu yada jita-jita na kokarin tada zaune tsaye, ta kuma bukaci ‘yan Najeriya su yi watsi da labaran bogi da ba su da tushe

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Fadar shugaban kasa ta yi magana kan rahotannin da ke cewa an maye gurbin Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

Fadar ta bayyana wannan labari a matsayin karya da yaudara ga al’umma kuma ba gaskiya ba ce ko kadan game da murabus dinsa.

Kara karanta wannan

'Ka ƙaƙaba mana dokar ta ɓaci kawai': Dattawan Arewa sun roƙi Tinubu alfarma

An ƙaryata cewa Akume ya yi murabus
Gwamnatin Tinubu ta ƙaryata ikirarin cewa Akume ya yi murabus. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hakan na cikin wata sanarwa da mai ba shugaban kasa shawara kan bayanai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a shafin X a daren jiya Asabar 28 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Labarin da ake ya yaɗawa kan Akume

Hakan ya biyo bayan yada jita-jita cewa Akume ya ajiye aikinsa kwana ɗaya bayan Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus.

Wasu na hasashen cewa Akume ya dauki matakin ne domin karbar shugabancin APC da ake tunanin daga yankin ya kamata ya fito.

Wasu har sun yada labarin cewa Hadiza Bala Usman aka nada a matsayin sabuwar sakataren gwamnatin tarayya.

A rahotannin da ake yaɗawa, an ce Bala Usman ta kafa tarihin zama mace ta farko da taba riƙe muƙamin a fadin Najeriya baki daya.

Babu gaskiya kan murabus din Akume
Gwamnatin Tinubu ta musanta labarin cewa Akume ya yi murabus. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Akume: Gwamnatin Tinubu ta magantu kan jita-jitar

Sai dai tun da wuri, fadar shugaban kasa ta yi gaggawar mayar da martani kan rade-radin domin cirewa al'umma shakku kan abin da ake yaɗawa.

Kara karanta wannan

'Ka cika gwarzo': Peter Obi ya yaba da murabus ɗin Ganduje, ya yi masa ruwan addu'o'i

Sanarwar ta sake tabbatar da cewa tsohon gwamnan Benue, Sanata Akume yana kan kujerarsa kamar yadda aka sani.

Har ila yau, ta tabbatar da cewa babu wani sabon nadi da aka yi na sakataren gwamnatin tarayya.

Sanarwar ta ce:

“Babu wani sauyi game da matsayin Mai Girma Sanata George Akume a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

'Babu nadin da Tinubu ya yi': Fadar shugaban kasa

Sanarwar ta kara da bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu, wanda ke kasar Saint Lucia a halin yanzu, bai nada wani sabon mukami ba.

Fadar shugaban kasa ta kira masu yada jita-jitar da “makiyan gaskiya” tare da bukatar ‘yan Najeriya su yi watsi da “labaran karya.”

Ganduje ya yi murabus daga shugabancin APC

Tun a farko, kun ji cewa tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan shekaru biyu a ofis.

An tabbatar da cewa an maye gurbinsa da mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa daga Borno, Bukar Dalori har zuwa lokacin babban taron jam’iyya da za a yi a Disamba.

Wannan matakin ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya da kuma rikice-rikicen cikin gida da ke kara ƙaruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.