Tinubu Ya Sake Ɗauko Mutumin Buhari, Ya ba Shi Babban Muƙami a Gwamnatinsa
- Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya naɗa tsohon hadimin Muhammadu Buhari mukami a gwamnatinsa domin kawo sauki ga al'umma
- Tinubu ya amince da nadin Ismael Ahmed a matsayin shugaban PCNGi domin rage wa ‘yan kasa raɗaɗin cire tallafin man fetur
- Ahmed zai jagoranci shirin samar da makamashi mai araha da tsafta, wanda ke ɗaya daga cikin hanyoyin tallafi da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake yin nade-nade a gwamnatinsa domin inganta ayyukan gwamnati.
Tinubu ya naɗa Ismael Ahmed a matsayin Shugaban zartarwa na shirin gas a fadar shugaban ƙasa (PCNGi) wanda ake sa ran na da alaƙa da cire tallafin mai.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata sanarwa da hadimin shugaban kasa a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X a yau Juma'a 27 ga watan Yunin 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wanene Ismael Ahmed da Tinubu ya ba muƙami?
Ahmed mai shekaru 45, ya kammala karatu daga Jami’ar Abuja inda ya sami digirin lauya a 2005.
Daga baya, ya tafi Jami’ar Webster da ke St. Louis, Missouri a Amurka, a nan ya karanci dangantaka ta duniya, sadarwa da diflomasiyya a 2008.
Ismael Ahmed ya taba zama hadimin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari kan shirin tallafi tsakanin shekarun 2018 zuwa 2022.
Sauyi da ake tunanin Ismael zai kawo a PCNGI
Ahmed zai jagoranci ayyukan wannan shiri na shugaban ƙasa, wanda aka kirkiro domin rage tasirin cire tallafin man fetur ta hanyar samar da makamashi mai rahusa.
PCNGi na ɗaya daga cikin shirye-shiryen tallafi da gwamnatin Tinubu ke aiwatarwa domin rage wa ‘yan ƙasa wahalar da cire tallafin ya janyo.

Source: Facebook
Martanin mutane da dama kan nadin Ismael
Mutane masu amfani da kafofin sadarwa musamman X sun yi martani inda wasu ke taya shi murna yayin da wasu sukar lamarin.
Lee Prince:
"Bayan sukarsu a gidan talabijin na Channels, yanzu an saka masa."
Crypt_Sali:
"Ina taya shi murna, ina fatan zai kawo karshen yawan layi a Abuja daga bisani zuwa sauran jihohi.
"Wannan shi ne shirin farko da ya kamata a yi amfani da shi yadda ya dace."
Olusola Omole:
"Mutum mai biyayya ga jam'iyya kuma mutumin kirki, wannan abin ya dace, ina taya ka murna."
Madu Jude:
"Wannan nadi ne da ya dace, ina taya shi murna.
"A hirarsa da gidan talabijin na Channels ya ce ko da muƙami ko babu a shirye yake ya yi aiki ga Tinubu."
Tinubu ya naɗa Dogara muƙami a kamfanin NCGC
A baya, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya kafa kamfanin ba da lamuni na kasa (NCGC), inda Yakubu Dogara ya zama shugaban kwamitin gudanarwa.
Kamfanin NCGC zai rage hadarin bayar da bashi ga kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa, matasa, mata da masana’antu don inganta tattali.
Har ila yau, kamfanin zai fara aiki a watan Yulin 2025, tare da goyon bayan Bankin Duniya da hukumomin MOFI, NSIA, BOI da CrediCorp.
Asali: Legit.ng

