'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Basarake a Jihar Bauchi

'Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Basarake a Jihar Bauchi

  • Ƴan bindiga sun yi ɓarna bayan wani harin ta'addanci da suka kai a jihar Bauchi da ke yankin Arewa maso Gabas
  • Miyagun ƴan bindigan sun yi awon gaba da wani basarake bayan harin da suka kai a ƙauyen Kanaka a ƙaramar hukumar Ganjuwa
  • Jami'an ƴan sanda sun bazama domin ƙoƙarin ceto basaraken mai shekara 56 da haihuwa a duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Bauchi - Ƴan bindiga sun tayar da hankula a jihar Bauchi bayan da suka yi awon gaba da wani basarake.

Ƴan bindigan waɗanda suka kai hari a ƙauyen Kanaka da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Ganjuwa a jihar Bauchi, sun sace dagacin ƙauyen, Abdullahi Ibrahim, wanda ke da shekaru 56 da haihuwa.

'Yan bindiga sun sace basarake a Bauchi
'Yan bindiga sun yi awon gaba da basarake a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Masanni kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun farmaki kauyukan Sokoto, an samu asarar rayuka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda ƴan bindiga suka sace basaraken

Wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa mummunan lamarin ya faru ne a ranar Laraba da misalin ƙarfe 1:15 na dare.

A cewar wata majiya ƴan bindigan sun iso ƙauyen cikin daren babu zato babu tsammani, suka zagaye gidan dagacin, sannan suka kutsa ciki tare da yin awon gaba da shi zuwa wani wuri da ba a sani ba har yanzu.

Bayan samun labarin sace dagacin, jami’an tsaro daga rundunar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar mafarautan gargajiya a yankin sun bazama domin aikin ceto.

Jami'an tsaron sun fara bincike tare da sintiri a dazuka da sauran wuraren da ake zargin za a iya ɓoye basaraken aka sace.

Wata majiya daga rundunar ƴan sanda ta tabbatar da cewa ana ci gaba da zurfafa bincike domin gano inda aka kai Abdullahi Ibrahim da kuma kama waɗanda ke da hannu a wajen sace shi.

Jami'an tsaro na bakin ƙoƙari

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: Jami'an DSS sun cafke rikakkun 'yan bindiga bayan dawowa daga Saudiyya

Majiyar ta ce rundunar za ta yi duk mai yiwuwa domin ganin an ceto shi cikin koshin lafiya ba tare da ya cutu ba.

Hukumomi da iyalan wanda aka sace sun shiga damuwa, yayin da jama'ar yankin ke bayyana damuwarsu da fargaba game da sake afkuwar irin wannan lamari a nan gaba.

'Yan bindiga sun sace basarake a Bauchi
'Yan bindiga sun yi ta'asa a Bauchi Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

An buƙaci jama'a da su ci gaba da bayar da hadin kai da kuma kai rahoton duk wani motsi da ba a saba gani ba ga jami'an tsaro domin a samu nasarar daƙile irin waɗannan laifuka.

Rundunar ƴan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da cewa ana gudanar da bincike a hukumance, kuma za a sanar da al’umma duk wani cigaba da aka samu a lamarin.

Ƴan bindiga sun kai hari a Sokoto

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu ƴan bindiga ɗauke da makamai sun kai hari a wasu ƙauyuka biyu na jihar Sokoto.

Miyagun ƴan bindigan sun hallaka mutane takwas a hare-haren da suka kai a ƙauyukan na ƙaramar hukumar Tangaza.

Rundunar ƴan sandan jihar Sokoto ta tabbatar da aukuwar harin wanda ƴan bindigan suka kai a ƙauyukan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng