1447: Saudiyya, Sarkin Musulmi Sun Yi Bayanin Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

1447: Saudiyya, Sarkin Musulmi Sun Yi Bayanin Shiga Sabuwar Shekarar Musulunci

  • Kotun Koli ta Saudiyya ta bayyana ranar Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, a matsayin farkon watan Muharram, alamar shiga sabuwar shekara
  • Sarkin Musulmi a Najeriya, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar, ya tabbatar da ganin jinjirin watan a sakonsa na ranar Laraba da dare
  • Ranar Ashura, wato 10 ga watan Muharram, za ta kasance a ranar Asabar, 5 ga Yuli, 2025, wacce ke da muhimmanci a addinin Musulunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Sabuwar shekarar Musulunci ta 1447AH ta fara a yau Alhamis, 26 ga Yuni, 2025, bayan da aka tabbatar da ganin jinjirin watan Muharram a daren Laraba a Saudiyya da Najeriya.

Kotun Koli ta Saudiyya ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar bayan tabbatar da ganin watan.

Kara karanta wannan

1447AH: Gwamna Radda ya ba da hutu don shigowar sabuwar shekarar musulunci

Musulman duniya sun shiga sabuwar shekara
Musulman duniya sun shiga sabuwar shekara. Hoto: Inside the Haramain
Source: Facebook

Shafin Saudiyya na Inside the Haramain ya wallafa a X cewa kwamitin ganin wata ya tabbatar da ganin jinjirin watan da yammacin ranar Laraba, 29 ga Zulhijja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A Najeriya, Kwamitin Duba Wata na Ƙasa da ke ƙarƙashin NSCIA ya tabbatar da hakan, inda ya ce Sarkin Musulmi ya amince da sahihancin ganin watan a wasu yankuna na ƙasar.

An sanar da shiga sabuwar shekarar Musulunci

Hukumomi sun tabbatar da cewa an tabbatar da ganin jinjirin watan Muharram a Saudiyya, kuma ranar Alhamis ce 1 ga Muharram 1447 AH.

Sanarwar da aka fitar ranar Laraba ta ce:

"Bayan tabbatar da ganin jinjirin watan Muharamma, gobe Alhamis za a shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447,"

A Najeriya kuwa, a cikin wani saƙo da kwamitin NMSC ta wallafa a X, an bayyana cewa:

"Mai Alfarma Sarkin Musulmi ya bayyana Alhamis, 26/6/2025, a matsayin 1 ga Muharram 1447 AH bayan an ga jinjirin wata"

Kara karanta wannan

1447: Jihohin Najeriya da suka ayyana hutu saboda shigowar sabuwar shekarar Musulunci

Sarkin Musulmi ya tabbatar da shiga sabuwar shekarar Musulunci
Sarkin Musulmi ya tabbatar da shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1447. Hoto: National Moon Sighting Committee
Source: Facebook

Muhimmancin Muharram da ranar Ashura

Watan Muharram na ɗaya daga cikin watanni huɗu masu alfarma a addinin Musulunci, inda aka hana yaki da rikici, tare da ƙarfafa ibada.

Ranar Ashura, wadda ke faruwa a ranar 10 ga Muharram, na ɗaya daga cikin ranakun da Musulmai ke darajawa sosai, musamman wajen azumi.

Ashura za ta zo ne a ranar Asabar, 5 ga Yuli, 2025, inda Musulmai za su gudanar da azumi da addu’o’i da sauran ayyukan ibada.

Tarihin kalandar Hijira ta Musulunci

Kalandar Hijira ko kalandar Musulunci ta samo asali ne daga hijirar Annabi Muhammad (SAW) daga Makkah zuwa Madinah.

Kalandar ta ƙunshi watanni 12, kuma kowanne wata yana farawa ne da ganin jinjirin wata, tsarin da ya bambanta da na Miladiyya.

Musulmai a fadin duniya na amfani da wannan kalanda wajen tsarawa da gudanar da bukukuwan addini kamar Ramadan, Hajj da sauran abubuwan ibada na Musulunci.

Kara karanta wannan

1447 AH: Gwamna Kirista ya ba da hutun sabuwar shekarar Musulunci a jiharsa

Mahajjatan Najeriya na dawowa daga Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa mahajjatan Najeriya sun fara dawowa gida bayan kammala aikin Hajjin shekarar 1446.

Shugaban hukumar alhazai ta kasa, Farfesa Abdullahi Sale Usman ne ya tabbatar da hakan wa manema labarai.

Farfesa Abdullahi Sale Usman ya bayyana cewa hukumar alhazai ta kasa ta samu gagarumar nasara a Hajjin shekarar 1446 da aka kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng