Duk da Ƙarƙare Yaƙin Iran da Isra'ila, Farashin Fetur Ya Tashi a Gidajen Man NNPCL

Duk da Ƙarƙare Yaƙin Iran da Isra'ila, Farashin Fetur Ya Tashi a Gidajen Man NNPCL

  • Kamfanin mai na kasa watau NNPCL ya ƙara farashin kowace litar man fetur zuwa N925 a jihar Legas inda ya fi araha
  • Wannan ƙari na zuwa ne kwanaki biyu kacal bayan kamfanin ya tashi farashin na man fetur zuwa sama da N900
  • A makon da ya gabata matatar hamshakin attajirin nan, Aliko Ɗangote ta ƙara nata farashin man feturin ga ƴan kasuwa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Lagos - Kamfanin da ke kula da harkokin mai na ƙasa wato NNPC, ya ƙara farashin kowace lita guda ta man fetur daga N915 zuwa N925 a jihar Legas.

Wannan ƙari na zuwa ne sa'o'i 48 bayan kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar fetur daga ƙasa da N900 zuwa N915.

Gidan man NNPCL.
A karo na biyu cikin sa'o'i 24, kamfanin NNPCL ya ƙara farashin litar fetur a Legas Hoto: NNPC Limited
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta lura da cewa tuni aka fara aiki da sabon farashin litar fetur watau N925 a gidajen sayar da mai mallakin NNPCL da ke Fin Niger, LASU Iba, da Igando duk a jihar Legas.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kunyata majalisar tarayya, ya ƙi sanya hannu a ƙudirin dokar NDLEA

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda NNPCL ya ƙara farashin fetur a Legas

Rahoton da aka tattara ya tabbatar da cewa kamfanin NNPCL ya yi ƙari na biyu a farashin litar man fetur, cikin awanni 48.

Tuni dai manyan masu ruwa da tsaki a masana’antar man fetur suka fara daidaita farashinsu sakamakon rashin tabbas a kasuwar danyen mai ta duniya.

Yakin da ya gudana tsakanin ƙasashen Iran da Isra'ila na ɗaya daga cikin dalilan da suka sa man fetur ya ƙara tsada sakamakon tashin farashin gangar ɗanyen mai a duniya.

Sai dai duk da an cimma matsayar kawo ƙarshen yakin, rahotanni daga Legas sun nuna cewa NNPCL ya ƙara farashin kowace lita zuwa N925 a gidajen mai.

A ranar 21 ga Yuni, Matatar Mai ta Dangote ta ƙara farashin man fetur a wurin da ƴan kasuwa ke lodi zuwa N880 kan kowace lita, rahoton Vanguard.

Matatar Ɗangote ta ɓullo da tsarin jigila

Kafin wannan karin, matatar ta Dangote ta bayyana shirinta na jigilar man fetur zuwa gidajen man ƴan kasuwa a fadin ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Gwamnan Benue ya fusata da kisan matafiya 'yan Kano, ya sha alwashi

Matatar ta ce ta sayi sababbin manyan motocin tanka 4,000 masu amfani da iskar gas (CNG) domin ƙarfafa damar isar da man a fadin Najeriya.

Sai dai, Kungiyar Ma'aikatan Gidajen Mai ta Ƙasa (PETROAN) ta ce wannan tsarin na matatar Dangote na iya mamaye kasuwar baki ɗaya, wanda kuma zai iya jawo rashin aikin yi.

NNPC ya kara farashin fetur a Legas.
Farashin man fetur na ci gaba da tashi a Najeriya duk da saukar ɗanyen mai a kasuwar duniya Hoto: Legit.ng
Source: Original

A ranar 19 ga Yuni, ƙungiyar manyan 'yan kasuwar mai ta Najeriya (MEMAN) ta bukaci a fito a yi karin haske kan yadda matatar Dangote ke shirin samar da hanyoyin jigilar fetur da dizal a faɗin ƙasa.

Sai dai ana tsaka da haka ne, aka wayi gari NNPCL ya sake ƙara farashin man fetur, duk da babu wata sanarwa a hukumance daga kamfanin.

Matatar Ɗangote ta ƙara farashin fetur

A wani rahoton, kun ji cewa Matatar Dangote da ke Legas ta ƙara farashin litar man fetur daga N825 zuwa N880.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da farashin danyen mai a kasuwannin duniya ya fara sauka bayan tashin da ya yi saboda yakin Iran da Isra'ila.

Ana ganin wannan ƙarin zai shafi gidajen mai musamman na Arewa, lamarin da masana ke ganin zai iya jawo tashin farashin kayayyaki a kasuwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262