Kwana 1 da Maganar Tsagaita Wuta, Isra'ila Ta Jajubo Gagarumin Zargi kan Iran
- Kasar Isra'ila ta sanya wani takunkumi kan Iran ana tsaka da tsagaita wuta tsakanin kasashen da ke fada da juna
- Isra'ila ta ayyana babban bankin Iran a matsayin ƙungiyar ta'addanci don hana kudi zuwa kungiyoyin da Iran ke tallafawa a Gabas ta Tsakiya
- Ministan tsaro a kasar ya ce wannan matakin na daga cikin yunkurin hana Iran hada-hadar kuɗi da ke taimaka wa ayyukan ta'addanci da rikice-rikice a yankin
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Tel Aviv, Israel - Yayin da ake ƙoƙarin kawo karshen rikici da Iran, Isra'ila tana neman mayar da aiki baya.
Ministan tsaron Isra’ila, Israel Katz a ranar Laraba ya ayyana babban bankin Iran a matsayin “kungiyar ta’adda”, yana cewa hakan na nufin dakile kudin ta’addanci ne.

Source: Getty Images
An shirya tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Iran
Wannan na daga cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba 25 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton Business Today.
Iran da Isra’ila sun amince da tsagaita wuta a ranar Talata, bayan kwana 12 na farmaki da martani tsakanin kasashen biyu masu gaba da juna.
Kasashen biyu sun daɗe suna yaki, inda Isra’ila ke yaki da kungiyoyin da Iran ke marawa baya kamar Hamas tun watan Oktoba 2023.
Isra’ila ta ce farmakin da ta fara a ranar 13 ga Yuni na hana Iran kera makamin nukiliya ne, da kasar ta sha musanta.
“Mun kammala wani babban mataki, amma ba mu gama da Iran ba. Mun shiga sabon mataki bisa nasarorin da muka samu."
- Cewar Eyal Zamir

Source: Getty Images
Trump ya magantu kan harin Amurka a Iran
Hakan ya biyo bayan shigar Amurka cikin yakin inda ta kai farmaki kan cibiyoyin nukiliyar Iran.
Shugaba Donald Trump ya ce hare-haren da sojojin Amurka suka kai sun rushe cibiyoyin nukiliyar Iran gaba ɗaya.
Ya bayyana hakan ne a taron shugabannin NATO da ke gudana a Netherlands, inda ya ce tsagata wuta tsakanin Iran da Isra'ila na tafiya daidai.

Kara karanta wannan
Wace ƙasa ta yi nasara tsakanin Iran da Isra'ila? Netanyahu ya yi jawabi bayan tsagaita wuta
Trump ya ce Iran ta harba manyan makamai da suka yi illa a kasar Isra'ila yayin da suka shafe kwanaki 12 suna gwabza yaki tsakaninsu.
Zargin ta'addanci da Isra'ila ke yiwa Iran
Minista Israel Katz ya sanya hannu a wani umarni na musamman da ya ayyana babban bankin Iran.
Har ila yau, daga cikinsu akwai wasu bankuna biyu da wani kamfani na sojojin Iran a matsayin kungiyoyin ta’adda, Punch ta ruwaito.
Sanarwar ta ce:
“Wannan yunkuri na daga cikin babban shirin yaki da Iran da ke nufin “cimma tsarin hada-hadar kudaden ta’addancin Iran da ke daukar nauyin kungiyoyi."
Isra'ila ta rasa sojojinta a Gaza
Kun ji cewa ana tsaka da maganar sulhu da Iran, kasar Isra'ila ta sanar da mutuwar sojojinta bakwai a Kudancin Zirin Gaza.
Hakan ya biyo bayan fashewar wani bam mai ƙarfi da ya tarwatse a motar da suke tafiya a cikinta wanda ya yi matukar taba Isra'ila a yankin.
An ce harin da Hamas ta ɗauki alhakinsa ya zama ɗaya daga cikin mafi muni ga sojojin Isra'ila a rikicin Gaza tun bayan barkewar fadan a 2023.
Asali: Legit.ng
