Natasha Ta Samu Matsala a Kotu, An Kori Karar da Ta Shigar kan Akpabio da Majalisa

Natasha Ta Samu Matsala a Kotu, An Kori Karar da Ta Shigar kan Akpabio da Majalisa

  • Kotun Daukaka Kara da ke Abuja ta ba da umarni na dakatar da sauraron karar da Godaswill Akpabio ya shigar kan Sanata Akpoti-Uduaghan
  • Wannan na zuwa ne a yayin da Natasha ke kalubalantar dakatarwar da Majalisar Dattawa ta yi mata, wanda ta ce ya saba doka da ka'ida
  • Kotun daukaka kara ta kuma bukaci a soke Shari'a mai lamba CA/ABJ/PRE/ROA/CV/395M/2025 dake gabanta

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kotun daukaka kara da ke Abuja ta bayar da umarnin dakatar da ci gaba da sauraron karar da Sanata Godswill Akpabio ya shigar a gaban Babbar kotun tarayya.

Kotun, ta yi umarnin a watsar da karar da aka shigar ranar 21 ga watan Mayun 2025, bayan ɓangaren Akpabio ya bukaci a janye karar da aka daukaka.

Kara karanta wannan

Gwamnati ta kammala shirin ranar dimokuradiyya, Tinubu zai yiwa kasa jawabi

Sanata Natasha da Godswil Akpabio
Natasha ta samu matsala a karar da ta shigar da Akpabio Hoto: Natasha H Akpoti/Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Premium Times ta wallafa cewa matakin ya biyo bayan roko da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya shigar yana neman ƙarin lokaci domin daukaka kara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Natasha ta maka Akpabio a kotu

Sahara reporters ta ruwaito cewa Sanata Natasha ta maka Shugaban Majalisar Dattawa da wasu mutum uku a kotu, inda take kalubalantar dakatarwar da aka yi mata ba.

Mai shari’a Obiora Egwuatu ya ba wa Akpabio da sauran wadanda ake karar sa’o’i 72 domin su bada amsa kan abin da zai sa a hana majalisa ci gaba da binciken Natasha.

Akpabio ya kalubalanci hukuncin kotu

Sai dai lauyoyin Akpabio karkashin babban lauya, Kehinde Ogunwumiju (SAN) suka shigar ranar 20 ga Maris, sun nemi karin lokaci domin daukaka kara.

Kotun daukaka kara ta amince da rokon Akpabio a ranar 21 ga Mayu, ta bayar da umarni da a dakatar da duk wasu harkoki na shari’a da ke gaban Babbar Kotun Tarayya har sai an kammala sauraron daukaka karar.

Kara karanta wannan

APC ta gyara kalamanta kan gargadin Sanata Ndume da ya caccaki gwamnatin Tinubu

Sanata Natasha Akpabio
Kori ta soke karar Natasha kan Akpabio Hoto: Natasha H Akpoti
Source: Facebook

Kwamitin alkalai uku da ya hada da Hama Barka, Adebukunola Banjoko, da Okon Abang, sun yarda da hujjar cewa ci gaba da shari’ar a kotun koli zai iya kawo nakasu.

Bayan haka, kotun ta ci Akpabio ya biya Natasha N100,000, tare da umarni da a goge karar da ke dauke da lamba CA/ABJ/PRE/ROA/CV/395M/2025 daga rajistar kotun.

'Ana son a tsige Sanata Natasha,' Lauya

A baya, mun ruwaito cewa wani daga cikin lauyoyin Natasha Akpoti-Uduaghan, ya zargi Gwamnatin jihar Kogi da goyon bayan yunkurin da ake yi na cire Sanatar daga kujerarta ta majalisar dattawa.

Victor Giwa, wanda ke cikin tawagar lauyoyin da ke kare Natasha, ya bayyana cewa ana amfani da al’amuran siyasa wajen ƙoƙarin cire Sanata saboda rashin jituwa da gillin siyasa.

A ranar 24 ga Maris, 2025, hadimar gwamnatin Kogi, Charity Omole ta jagoranci wasu daga cikin mazauna Kogi ta Tsakiya zuwa ofishin INEC domin mika korafi na neman yiwa Natasha kiranye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng