Gwamna Bago Ya ba da Tallafi ga Mutanen da Ambaliya Ta Ritsa da Su a Neja
- Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya tuna da mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a garin Mokwa
- Mai girma Umaru Bago ƴa ba da tallafin N1bn domin ragewa mutanen da ibtila'in ya shafa raɗaɗin abin da ya faru
- Gwamnan ya kuma ba da kwangiƙar ayyukan da za su laƙume N7bn domin samar da ababen more rayuwa a yankin
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Neja - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya ba da tallafi ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a garin Mokwa.
Gwamna Bago ya bayyana ibtila’in a matsayin wata masifa da jihar Neja da ma ƙasa baki ɗaya ba za su iya jure faruwar ta sau biyu ba.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa gwamnan ya bayyana hakan ne yayin ziyarar da ya kai garin Mokwa wanda ambaliyar ruwan ta shafa.
Gwamna Umaru Bago ya ba da tallafin N1bn
A yayin ziyarar Gwamna Bago ya yi alƙawarin cewa za a gaggauta ɗaukar matakai na sake tsugunar da duk waɗanda ambaliyar ta shafa.
A ziyarar da ya kai sansanin wucin gadi da ke makarantar firamare ta Tiffin Madza, inda daruruwan ƴan gudun hijira ke zaune, gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta bayar da tallafin N1bn.
Gwamnan ya kuma haɗa da motoci 50 ɗauke da nau’o’in hatsi domin taimaka wa waɗanda ambaliyar ta shafa, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.
A wani mataki na ƙara gyara ababen more rayuwa a yankin, gwamnan ya sanar da bayar da kwangilar aikin hanyar Mokwa-Raba, wanda ya haɗa da gina sababbin gadoji huɗu, a kuɗin da ya kai Naira biliyan 7.
Gwamna Bago ya gargaɗi mazauna yankin da su guji gina gidaje a kan hanyoyin ruwa, yana mai jaddada cewa irin waɗannan gine-gine suna ƙara tsananta illar ambaliya.

Kara karanta wannan
Gwamna Zulum ya tuna da iyalan sojojin da suka rasu a fagen daga, ya ba su tallafi
Ya bayyana cewa ma’aikatar filaye ta jihar ta samu umarni da ta fitar da takardar mallakar fili ga gwamnatin tarayya domin sauƙaƙa tsugunar da waɗanda ambaliyar ta raba da muhallinsu a wuri na dindindin.
"Gwamnati na da cikakken niyyar dawo muku da natsuwa da rayuwa mai inganci kamar yadda kuka saba."
“Komai da ya faru ƙaddara ce daga Allah, kuma Allah zai sauƙaƙa wa jama’a wannan mawuyacin lokaci."
“Zamu fara gina magudanan ruwa da gadaje na dindindin a cikin garin Mokwa domin hana sake afkuwar irin wannan masifa."
- Gwamna Umaru Bago

Source: Facebook
Bago ya sha alwashi kan kuɗaɗen da aka ba da
Gwamnan ya tabbatar da cewa duk kuɗaɗe da kayan agaji da gwamnatin tarayya, mutane masu zaman kansu da ƙungiyoyin bayar da tallafi suka bayar, za a yi amfani da su bisa gaskiya da adalci.
Ya nuna godiya ga duk mutanen da suka bada taimako ga waɗanda wannan annoba ta shafa, tare da roƙon sauran ƴan Najeriya da su ci gaba da goyon bayan waɗanda ambaliya ta yi wa illa.
Gwamna Bago ya hana hawan Sallah
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago ya hana gudanar da hawan Sallah.
Gwamna Bago ya ba da umarnin ne sakamakon ibtila'in ambaliyar ruwan da ta auku a garin Mokwa.
Umaru Bago ya nemi duka masarautu da sauran al'umma su yi haƙuri su taƙaita shagalin sallah duba da halin da jihar ta tsinci kanta a ciki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

