Shugaban NAHCON Ya ba Alhazai Shawara kan Shugabannin Najeriya
- Shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya yi kira ga Alhazan Najeriya da ke ƙasa mai tsarki.
- Farfesa Abdullahi Usman ya buƙaci Alhazan da su yi wa shugabanni addu'a domin su gudanar da jagoranci nagari
- Shugaban na NAHCON ya kuma yi kira ga Alhazan da su kasance masu ɗaukar darasi kan yadda malamai a Saudiyya suke sanya shugabanni cikin addu'a
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Saudiyya - Shugaban hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Usman, ya yi muhimmin kira ga Alhazan Najeriya.
Farfesa Abdullahi Usman ya buƙaci Alhazan da su yi wa ƙasa addu’a tare da neman Allah ya ɗora shugabanni kan hanya domin su iya gudanar da mulki nagari.

Source: Twitter
Farfesa Abdullahi Usman ya yi wannan kira ne a yayin da ya kai ziyara ga alhazan Najeriya daga jihohin Arewa maso Yamma a sansanoninsu da ke Mina, Saudiyya, a ranar Asabar, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
Hajjin 2025: Mahajjaci ɗan Najeriya ya rasu a wuri mai daraja da albarka a Saudiyya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban NAHCON ya buƙaci a yi addu'a
A cewarsa, jagorancin Allah yana da matuƙar muhimmanci wajen cimma nasarar shugabanci da ci gaban ƙasa, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Shugaban NAHCON ya buƙaci ƴan Najeriya da su ɗauki darasi daga ƙasar Saudiyya, inda malamai ke yawan addu’a ga shugabanninsu.
Ya ce irin wannan goyon bayan ta wajen yin addu'o'i yana da rawar da yake takawa a ci gaban ƙasar.
"Nasarar shugabanninmu ita ce nasarar ƙasarmu. Dole ne mu roƙa musu alheri, domin duk abin da muka roƙa musu mai kyau ko mara kyau, ƙasar ce zai shafa."
- Farfesa Usman Abdullahi
Farfesa Usman Abdullahi ya bayyana cewa ziyarar da suka kai na da nufin tantance walwalar Alhazan, samun sahihin bayani kai tsaye daga gare su, da kuma ɗaukar matakin da ya dace don gyara inda ya kamata.
Ya kuma shawarci Alhazan da su zama jakadun ƙasa nagari ta hanyar bin dokokin ƙasar da ke masaukinsu, tare da tunatar da su cewa ya zama dole su kasance da katin shaidarsu a kowane lokaci.

Kara karanta wannan
An kaɗa hantar Shugaba Tinubu kan matsalar tsaro, da yiwuwar a kifar da APC a zaben 2027
Ya yaba da yadda aikin Hajjin 2025 ke tafiya, inda ya danganta nasarar da haɗin gwiwa tsakanin masu ruwa da tsaki.

Source: Twitter
An yabawa hukumar NAHCON
A nasa bangaren, Amirul Hajj na jihar Katsina kuma mataimakin gwamna, Faruk Lawal, ya yaba da ƙoƙarin hukumar NAHCON.
Sai dai Faruk Lawal ya roƙi a samu tsarin biza guda ɗaya domin rage jinkiri da kuma inganta tsarin.
Haka nan, kwamishinan ayyuka, bincike da lasisi na NAHCON, Anofiu Elegushi, ya shawarci Alhazan da su guji ɗaukar kaya fiye da ƙima.
Anofiu Elegushi ya bayyana cewa kowanne Alhaji zai karɓi lita biyar na ruwan Zamzam, don haka babu buƙatar ɗaukar ruwa a cikin kayansu.
Ranar da Alhazan Najeriya za su dawo gida
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Alhazai ta ƙasa (NAHCONf ta bayyana lokacin fara jigilar dawo da Alhazai zuwa gida Najeriya.
Hukumar NAHCON ta bayyana cewa za a fara dawo da Alhazai zuwa gida Najeriya daga ranar, 13 ga watan Yunin 2025.
Shugaban hukumar NAHCON ya kuma taya Alhazan Najeriya murnar kammala aikin Hajji na shekarar 2025.
Asali: Legit.ng