Rigimar Sarauta Ta Ɓarke da Dakataccen Sarki Ya Kutsa Fada domin Ƙwace Kujerarsa

Rigimar Sarauta Ta Ɓarke da Dakataccen Sarki Ya Kutsa Fada domin Ƙwace Kujerarsa

  • Rikicin sarauta ya sake barkewa a kauyen Muye, ta jihar Niger, bayan tsohon dagacin kauyen ya koma fada da karfi domin kwace kujerarsa da aka hana shi
  • Rikicin ya kara kamari a ranar Juma'a 6 ga watan Yunin 2025 bayan magoya bayan bangarorin biyu sun yi artabu, lamarin da ya tayar da hankula
  • Jami'an tsaro sun shiga tsakani da gaggawa, kuma sun tabbatar da cewa an samu daidaito, yayin da ake cigaba da sa ido a yankin don wanzar da zaman lafiya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lapai, Niger - An shiga tashin hankali a jihar Niger da rigimar sarauta ta rikice bayan artabu tsakanin wasu ɓangarori da ke gaba da juna sanadin sarautar.

Rikicin masarautar ya sake kunno kai a kauyen Muye, karamar hukumar Lapai ta jihar Niger, inda magoya bayan bangarori biyu suka barke da fada.

Kara karanta wannan

'Ina Katsina, Zamfara?: An taso malaman addini a gaba kan kiran dokar ta ɓaci a Benue

An yi artabu kan kujerar sarauta a Niger
An rikice a Niger da dakataccen Sarki ya kutsa fada. Hoto: Legit.
Source: Original

An yi arangama kan rigimar sarauta a Niger

Rahoton Zagazola Makama ya tattaro cewa rikicin ya fara ne da misalin karfe 6:20 na yammacin ranar Alhamis 5 ga watan Yunin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya faru ne lokacin da aka tsige dagaci sannan kuma ya dawo da karfi domin darewa kujerarsa bayan dakatar da shi da aka yi.

An ce Alhaji Mohammed Abdulkadir Maigari II ya balle kofar fada ne bayan dawowarsa, lamarin da ya tayar da hankalin mazauna garin wanda ya rikide ya koma rikici.

Rikicin ya kara kamari bayan magoya bayan sabon Sarkin sun fuskanci tsohon dagacin kauyen saboda kokarin sake dawowa kan kujerar.

Amma jami’an tsaro sun shiga lamarin inda suka daidaita al’amura kafin aka samu kwanciyar hankali.

Jami'an tsaro sun dakile rigimar sarauta a Niger
Rigima ta ɓarke da Sarki ya kutsa fada domin ƙwace kujerarsa a Niger. Hoto: Mohammed Umaru Bago.
Source: Twitter

Yadda rigimar sarauta ta dawo a Niger

Sai dai daga baya an samu rahoton cewa da safiyar Juma’a rikicin ya sake tashi, inda aka yi arangama tsakanin magoya bayan bangarorin.

Kara karanta wannan

Ana tsaka da shagalin Sallah, mutane sun tafka asarar biliyoyin Naira a jihar Kano

Wannan fadan ya janyo rudani da tarwatsewar zaman lafiya a cikin al’umma, lamarin da ya sa aka sake aika jami’an tsaro.

“Hadakar jami’an tsaro sun daidaita lamarin, ana cigaba da sanya ido domin hana sake barkewar sabon rikici a yankin tare da tabbatar da kawo zaman lafiya a garin."

- Cewar wata majiya ta tsaro

Babu wani tabbacin asarar rai ko kama wasu mutane da ake zargi da hannu kan lamarin da aka tabbatar da shi a hukumance zuwa lokacin hada wannan rahoto

Niger: An cafke basarake kan zargin ta'addanci

Mun ba ku labarin cewa rundunar ƴan sanda a Niger ta cafke wani basarake da wasu mutum 13 bisa zargin taimakawa 'yan bindiga a garin Mashegu da ke jihar a Arewacin Najeriya..

An kama su ne a ranar 23 ga Mayun 2025 yayin wani samame da jami'an tsaro suka kai sansanonin 'yan bindiga a Guiwa da Telle wanda aka gano wasu makamai.

Rahotanni sun ce an gano babura huɗu, harsashi, da shanu 10 a gidan dagacin, yayin da bincike ke cigaba don gano sauran masu hannu a ta'addanci da ya addabi al'ummar jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.