Ana tsaka da Shagalin Sallah, Mutane Sun Tafka Asarar Biliyoyin Naira a Jihar Kano
- An tafka asarar dukiya da kadarori na biliyoyin Naira da gobara ta kama a kasuwar sayar da wayoyi watau Farm Centre a Kano
- Rahotanni sun tabbatar da cewa aƙalla shaguna 300 gobarar ta babbake da safiyar ranar babbar sallah, Juma'a 6 ga watan Yuni, 2025
- Shugaban kasuwar ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce an yi asara mai ɗumbin yawa musamman a ɓangaren shagunan sayar da wayoyi da kayan gyara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gobara ta tashi ta kone shaguna da dama a kasuwar wayoyi da ke Kano, wadda aka fi sani da Farm Centre, a safiyar ranar babbar Sallah.
Lamarin ya fara karade kafafen sada zumunta ne bayan wani ya wallafa bidiyo da ke nuna hayaki mai yawa na tashi daga wani bangare na kasuwar.

Kara karanta wannan
Hankula sun tashi da wani Musulmi ya mutu a wani irin yanayi bayan dawowa daga idi

Source: Original
Duk da yake har yanzu ba a bayyana musabbabin tashin wutar ba, ganau sun shaida wa Leadership cewa gobarar ta shafi shagunan da ke sayar da wayoyi da kayan haɗi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda wuta ta kama a kasuwar wayoyi a Kano
Wani dan kasuwar Farm Centre Muhammad Daula, ya bayyana cewa galibin masu shaguna ba su fito ba saboda yau take sallar layya.
Ya ce sai da abin ya fara yaɗuwa a kafafen sada zumunta sannan ƴan kasuwar suka samu labarin abin da ya faru.
"Mafi yawanmu ba mu je kasuwa ba yau saboda Sallah. Bidiyon da aka yada ne ya jawo hankalinmu muka gane abin da ke faruwa. Shaguna da ke kusa da nawa sun kone, abin ba daɗi," in ji shi.
Duk wani ƙokari da aka yi don jin ta bakin mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf, bai yi nasara ba, domin ba ya ɗaga waya.

Kara karanta wannan
Tsohon mawakin gargajiya a Najeriya ya rasu, Atiku da gwamna Mbah sun yi ta'aziyya
Ƴan kasuwar sun yi asarar biliyoyin Naira
Da aka tuntuɓe shi, shugaban kasuwar wayoyi ta Farm Centre da ke Kano, Jamilu Bala Gama ya shaida wa BBC cewa gobarar ta kwashe sa'o'i shida zuwa bakwai tana ci.
A cewar, wutar ta kama rigi-rigi tun kafin a ankara kuma ta taɓa shaguna sama da 300, amma ya ce ta fi kama ɓangaren masu sayar da wayoyin hannu da kayan gyara.

Source: Twitter
Jamilu Bala ya ce:
"Ba karamar barna wutar ta yi ba domin an yi asarar dukiya mai tarin yawa, za ka samu shago mai kayan Naira miliyan 500, wani Naira biliyan 1 amma duk sun ƙone."
Matasa 2 sun faɗa rami a jihar Kano
A wani labarin, kun ji cewa hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da rasuwar matasa biyu bayan sun fada rafi a gefen hanyar Ring Road, a gaban Dorayi Babba.
Rahotanni sun bayyana cewa matasan sun je karɓo bashin kudin da suke bi ne lokacin da ajali ya riske su a cikin birnin Kano.
Wadanda lamarin ya rutsa da su sune Saifullahi Muhammad mai shekaru 27 da Halifa Abdullahi mai shekaru 29, dukkansu mazauna unguwar Gwammaja ne.
Asali: Legit.ng