Najeriya Ta Yi Babban Rashi, Tsohon Alkalin Alkalai Mohammed Uwais Ya Rasu
- Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Uwais, ya rasu da safiyar ranar Juma’a yana da shekara 88 a duniya
- Uwais ya jagoranci kotun koli daga shekarar 1995 zuwa lokacin ritayarsa a 2006 sannan ya shugabanci kwamitin gyaran zabe
- An bayyana rasuwarsa ne ta bakin kwamishinan shari’a na Ondo, Dr Kayode Ajulo, wanda ya ce Uwais ya bayar da gagarumar gudumawa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon Alkalin Alkalan Najeriya, Mohammed Lawal Uwais, ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 88.
Rahotanni sun tabbatar da cewa kwamishinan shari’a na Jihar Ondo, Dr Kayode Ajulo ne ya fitar da labarin rasuwar shi.

Source: Twitter
Daily Trust ta rahoto cewa Mohammed Uwais ya rasu ne da safiyar ranar Juma’a 7 ga watan Yuni, 2025, bayan ya shafe lokaci mai tsawo yana taka rawar gani a fannin shari’a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Uwais ya jagoranci kotun koli a shekaru 11
Punch ta wallafa cewa Mohammed Uwais ya hau kujerar Alkalin Alkalan Najeriya a shekarar 1995, inda ya yi aiki har zuwa shekarar 2006 kafin ya yi ritaya.
A lokacin shugabancinsa, an samu sababbin tsare-tsare da ƙa’idojin da suka tabbatar da zaman lafiya da adalci a kotunan Najeriya.
Dr Kayode Ajulo ya bayyana cewa:
“Fitowata ta farko a kotu a matsayina na lauya ita ce a gaban kotun koli lokacin mai shari'a Uwais. Halayyarsa ta mutunci da gaskiya ta zama abin koyi ga al’umma baki ɗaya.”
Ya kara da cewa Uwais ya zama fitila ga tsarin shari’ar Najeriya, kuma ya tsaya tsayin daka wajen ganin an kare gaskiya da adalci a kowanne mataki na kotu.
Uwais ya jagoranci gyaran tsarin zaben Najeriya
Bayan ritayarsa, Uwais ya shugabanci Kwamitin Gyaran Zabe na Ƙasa da marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ya kafa domin duba matsalolin da ke addabar tsarin zabe.
Kwamitin ya kunshi manyan mutane kamar Bishop Matthew Hassan Kukah da lauyan kare hakkin ɗan Adam, Dr Olisa Agbakoba (SAN).

Source: UGC
An ruwaito cewa kwamitin ya gabatar da shawarwari masu muhimmanci da suka hada da kafa hukumar zabe mai cikakken ‘yanci.
Hakanan, kwamitin Uwais ya goyi bayan amfani da fasahar zamani wajen gudanar da zabe da kuma isar da sakamako ta intanet domin rage maguɗi da inganta sahihancin zabe a Najeriya.
Uwais ya ba dimokuraɗiyya gudumawa
Rahotanni sun bayyana cewa wasu daga cikin shawarwarin da Uwais ya bayar na ci gaba da taka rawa a tsarin zabe da dimokuraɗiyyar Najeriya har zuwa yau.
Ya kuma bayar da gudunmawa wajen inganta ilimin masu kada ƙuri’a da tsarin kashe kuɗi tsakanin jam’iyyu.
Farfesa Jibril Aminu ya rasu
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon Sanata daga jihar Adamawa, Farfesa Jibril Aminu ya rigamu gidan gaskiya.
Farfesa Jibrin Aminu ya kasance cikin fitattun masana lafiya a Najeriya da ya yi aiki a matakai daban daban.
Legit ta rahoto cewa marigayin ya rike manyan mukamai a ciki da wajen Najeriya ciki har da ministan ilimi da man fetur.
Asali: Legit.ng

