Barawo Ya Fada Kogi Ya Mutu Yana Kokarin Gudu bayan Fizge Jakar Wata Mata

Barawo Ya Fada Kogi Ya Mutu Yana Kokarin Gudu bayan Fizge Jakar Wata Mata

  • Wani matashi da ake zargin mai satar jaka ne ya nutse ya mutu a kogin Asa a Ilorin yayin da yake tserewa daga wajen aikata laifi
  • Shaidun gani da ido sun ce ya sace jakar wata mata da ke cikin Keke Napep ne, ya gudu ya fada cikin kogin don tserewa jama’a
  • Bayan kokarin ceto shi ya ci tura, an gano gawarsa a gefen kogin da ya nutse bayan kusan awa biyu da afkuwar lamarin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara - Wani matashi ya rasa ransa bayan da ya nutse a kogin Asa da ke cikin birnin Ilorin, babban birnin jihar Kwara, yayin da yake tserewa daga wajen da ya fizge jaka.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 2:30 na rana a ranar Talata a unguwar Emir’s Road da ke cunkushe da jama’a.

Kara karanta wannan

Yadda aka zabga wa Sarki lafiyayyen mari a taron da gwamnan Ondo ya kaddamar da titi

Barawo ya musu yana kokarin gudu a Kwara
Dan fizge ya fada Kogi ya mutu a Kwara. Hoto: Legit
Source: UGC

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa lamarin ya faru ne a lokacin da ya sace jakar wata mata da ke cikin babur mai kafa uku, wanda aka fi sani da Keke Napep.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahotanni sun bayyana cewa matashin da ake kyautata zaton dan shekaru 20 da haihuwa ne ya yi yunkurin tserewa ta hanyar tsallakawa cikin kogin Asa, amma hakan ya zama ajalin shi.

Dan kwace ya fada kogi yana kokarin gudu

Wani ganau mai suna Gada ya bayyana cewa matashin ya yi gaggawar tserewa bayan satar jakar, inda ya haye titi ya kuma fada cikin kogin Asa da ke kusa da wajen.

Rahotanni sun tabbatar da cewa matashin ya cika rigarsa da iska ne domin tserewa wadanda suka fara rige-rigen kamashi.

Trust Radio ya wallafa cewa Gada ya ce:

“Ya dauki jakar ya gudu. Mutane suka fara ihu. Kafin ma wani ya tashi ya riga ya fada cikin kogin.

Kara karanta wannan

'Zan kare kai na': An hango Sheikh Bello Yabo dauke da bindiga a wajen Wa'azi

"Mun tsaya ba tare da sanin abin da za mu yi ba. Wasu sun kokarta su taimaka, amma kokarinsu ya ci tura."

Shaidun gani da ido sun ce duk da kokarin wasu da suka tsaya wajen da abin ya faru domin neman ceto shi ya gagara saboda rashin ganin shi a ruwan.

Sun kara da cewa gawarsa ta ki bayyana sai bayan kusan awa biyu da afkuwar lamarin, inda aka gano ta kwance a bakin kogin.

Hukuma ta tabbatar da mutuwar mai kwace

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kwara, Hassan Adekunle, ya tabbatar da aukuwar lamarin lokacin da manema labarai suka tuntube shi a ranar Laraba.

Sai dai ya bayyana cewa ba hukumar ce ta ceto gawar ba, yana mai cewa:

“Mun samu rahoton hadarin, amma ba mu muka jagoranci aikin daukar gawar ba.”
Ba a samu bayanin 'yan sanda kan mutuwar barawo a Kwara ba
Ana jiran bayanin 'yan sanda mutuwar barawo a Kwara. Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Har zuwa lokacin da aka samu rahoto daga wajen da lamarin ya faru, babu wata sanarwa daga rundunar ‘yan sanda a jihar game da matakin da za a dauka.

Mutane 7 sun mutu a kogin Sokoto

Kara karanta wannan

Hako mai a Arewa: Jihar Neja na neman hadaka da Dangote kan samar da fetur

A wani rahoton, kun ji cewa an samu hadarin jirgin ruwa a wani kogi a karamar hukumar Shagari a Sokoto.

Jami'an hukumar NEMA sun kai agajin gaggawa tare da tabbatar da cewa iska mai karfi ce ta jawo hadarin.

Bayan zuwa bakin kogin, hukumar NEMA ta ziyarci iyalan mutane bakwai da suka rasa rayukansu a sanadiyar hadarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng