Haka Allah Ya So: Martanin Sarkin Gwandu da Kotu Ta Tabbatar da Tsige Shi daga Sarauta

Haka Allah Ya So: Martanin Sarkin Gwandu da Kotu Ta Tabbatar da Tsige Shi daga Sarauta

  • Sarkin Gwandu, Al-Mustapha Jokolo ya amince da hukuncin kotu bayan shekaru 20 yana kalubalantar tsige shi
  • Tsohon Sarkin ya kalubalanci nadin Alhaji Iliyasu Bashar Al-Mustapha, wanda ya maye gurbinsa a sarautar Kebbi
  • Kotun koli ce dai ta kawo karshen rikicin masarautar, bayan ta soke hukuncin babbar kotun jihar Kebbi da ya maido shi

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kebbi – Lauyan tsohon Sarkin Gwandu, Al-Mustapha Jokolo, ya ce sun amince da hukuncin Kotun Koli da ta rushe hukuncin dawo da Jokolo kan karagar mulki.

A hukuncin da kotun koli ta yanke, ta ce babbar kotun jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron karar, domin ba a bi sharuddan da doka ta gindaya ba kafin shigar da ita.

Kara karanta wannan

Gwandu: Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta raba gardama kan rigimar sarauta

Tsohon Sarkin Gwandu ya hakura
Tsohon Sarkin Gwandu, Jogolo ya ce ba zai sake waiwayar hukuncin kotu ba Hoto: Surajo Muhammad
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun koli ta kuma tabbatar da Alhaji Muhammadu Iliyasu Bashar a matsayin halastaccen sarkin Gwandu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta kawo ƙarshen rikicin sarautar Gwandu

21 Century Chronicles ta wallafa cewa wannan hukunci, ya kawo ƙarshen rikicin da ya ɗauki shekaru 20 tsakanin Iliyasu Bashar da Al-Mustapha Jokolo kan sarautar Gwandu.

Bashar, wanda ɗan uwan Jokolo ne, ya kalubalanci hukuncin da ke son dawo da tsohon Sarkin sarauta ta hannun lauyansa, Yakubu Maikyau (SAN), wanda ya shigar da ƙara a madadinsa da gwamnatin Kebbi.

An shafe shekaru Kan rikicin masarautar Gwandu
Tsohon Sarkin Gwandu, Jogolo ya ba jama'a Hakuri Hoto:Legit.ng
Source: Original

A martaninsa kan hukuncin, lauyan Jokolo, Sylvester Imhanobe, ya ce ba za su nemi sake duba hukuncin ba domin Jokolo ya amince da hukuncin tare da tawali’u.

Sai dai Imhanobe ya bayyana mamaki kan yadda yawancin alkalan suka jingina hukuncinsu da sashe na 4 na dokar nada da tsige sarakuna a Jihar Kebbi.

Ya ce karar da suka shigar tana karkashin sashe na 6 wanda ba ya buƙatar ƙorafi kafin a garzaya kotu, saboda ba batun zaɓen sabon sarki bane.

Kara karanta wannan

Jirgin ruwa ya kife da mutane a tsakiyar kogi a Sokoto, an rasa rayuka

Kotu: Sarki Jokolo ya ba masoya hakuri

Wani na kusa da Jokolo ya shaida cewa tsohon sarkin ya roƙi magoya bayansa da su ɗauki hukuncin a matsayin kaddara daga Allah. Majiyar da ta nemi a sakaya sunanta ta ce Jokolo ya kuma bukaci magoya baya da su kwantar da hankalinsu, kar su ji komai a kan hukuncin. A cikin hukuncin da Mai Shari'a Emmanuel Agim ya gabatar, kotun koli ta ce ya kamata ya Jokolo ya shigar da ƙorafi a hukumance zuwa wajen gwamna.

Ya ce wannan shi ne tanadin doka a sashe na 4 ya umarci a bi kafin ya garzaya kotu a kan batun masarautar.

Kotu ta yi hakunci kan dambarwar Sarauta

A wani labarin, mun wallafa cewa kotun koli ta yanke hukunci kan rikicin sarautar Gwandu, inda ta soke dawowar Al-Mustapha Haruna Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu.

A ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025, Mai Shari'a Emmanuel Agim ya bayyana cewa kotun jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron ƙarar da Jokolo ya shigar gabanta.

Kotun Ƙoli ta soke dukkannin hukuncin da kotun jiha da na ɗaukaka ƙara suka yanke a baya, tana mai tabbatar da cewa Jokolo ba zai dawo kan kujerar sarautar Gwandu ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng