Bola Tinubu Ya Karɓi Bakuncin Fitaccen Malami, Tunde Bakare, An Ji Abin da Suka Tattauna
- Fitaccen malamin kirista wanda ya kafa cocin Citadel Global Community Church, Fasto Tunde Bakare ya ziyarci Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas
- Rahoto ya nuna cewa Fasto Tunde Bakare, wanda ɗan jam'iyyar APC ne ya tattauna muhimman batutuwa da shugaban ƙasa, Bola Tinubu
- Bakare yana ɗaya daga cikin ƴan takarar da suka fafata a zaben fidda gwani na jam'iyyar APC gabanin zaɓen 2023, wanda Tinubu ya samu nasara
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Lagos - Shugaban Cocin Citadel Global Community Church, Tunde Bakare, ya kai ziyara ta girmamawa ga Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas
Babban malamin ya gana da Shugaba Tinubu kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa yau Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025.

Source: Twitter
Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da wallafa a shafinsa na X.
Onanuga ya ce:
"Fasto Tunde Bakare ya kai iyara ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a jihar Legas, yau Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025."
Me ya kai Fasto Tunde Bakare wurin Tinubu?
Rahotanni sun ce ziyarar ta mayar da hankali ne kan muhimman batutuwan kasa da kuma halin da Najeriya ke ciki a halin yanzu.
A baya, yayin wani jawabi da ya gabatar a cikin watan Afrilu a Legas, Bakare ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dauki matakan gaggawa da dabaru domin ceto Najeriya daga cikin matsalolin da ke addabar ta.
Malamin addinin ya jaddada cewa akwai buƙatar bullo da tsare-tsare masu inganci da za su amfani jama'a domin ceto ƙasar nan daga halin ƙaƙanikayin da ta shiga.
Fasto Tunde Bakare ya yi takara da Buhari
Bakare ya kasance tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, ya yi takara tare da Muhammadu Buhari a zaben 2011 a karkashin inuwar jam’iyyar CPC.
A shekarar 2022, fitaccen malamin cocin ya sayi fom din neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC mai mulki a kan Naira miliyan 100.
Sai dai, bai samu kuri’a ko daya ba a zaben fidda gwani na jam’iyyar APC da aka gudanar a Abuja a 2022.

Source: Getty Images
Shugaba Bola Tinubu ne ya lashe zaben fidda gwanin, inda ya samu kuri’un deleget 1,217, ya doke sauran ‘yan takara baki daya.
A halin yanzu dai babu wata sanarwa da ta bayyana maƙasudin wannan ziyara da Fasto Tunde Bakare ya kai wa Tinubu amma bayanai sun nuna cewa sun tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban ƙasa.
Fubara ya gana da Bola Tinubu a Legas
A wani labarin, kun ji cewa gwamnan jihar Ribas da aka dakatar, Sir Siminalayi Fubara ya kai ziyara ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a Legas.
Fubara ya gana da Shugaba Bola Tinubu ne a gidansa da ke jihar Legas, a ranar Talata, 3 ga watan Yunin 2025.
Wannan ganawar na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin sulhunta gwamnan da tsohon uban gidansa a siyasa, ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

