Gwamna Ya Karrama Jami'in NIS da Ya ki Karbar N10m wajen Bokan da aka Kama
- Gwamna Alex Otti na Abia ya yaba da gaskiya da rikon amana da wani jami’in hukumar shige da fice ya nuna wajen ƙin karɓar cin hancin Naira miliyan 10
- Jami’in NIS, Ugochukwu Orji, ya ƙi karɓar kuɗin da wani boka da ake zargi da kisan gilla ya bayar yayin da yake ƙoƙarin tserewa daga Najeriya
- Rahoto ya nuna cewa gwamna Otti ya ce wannan hali na gaskiya da amana na wakiltar dabi’un mutanen Abia na kirki da ƙin aikata laifi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Abia - Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya jinjinawa wani jami’in hukumar shige da fice ta ƙasa (NIS), Ugochukwu Orji, bisa ƙin karɓar hancin Naira miliyan 10 daga hannun wani boka.
Legit ta rahoto cewa ana zargin bokan da aikata kisan gilla da ayyukan asiri da suka hada da birne mutane a jihar Enugu.

Kara karanta wannan
Bayan ganawa da wakilan gwamnati, ma'aikatan shari'a sun amince a janye yajin aiki

Source: Twitter
Mai magana da yawun gwamnan jihar Abia, Njoku Ukoha ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Otti ya yi wannan yabon ne a ranar Lahadi yayin da ya karɓi tawagar mutum 30 da suka shirya taron girmamawa da godiya da aka yi wa jami'in a Isiala.
Otti ya yabi wanda ya ki karbar kudin boka
A cewar Gwamna Otti, kudin suna da yawan gaske kuma ya kamata a jinjinawa duk wanda ya ki karbarsu.
Premium Times ta wallafa cewa gwamnan ya ce:
“Naira miliyan 10 kuɗi ne da za a iya yin abubuwa da dama da su, amma ka ƙi karɓarsu saboda ba naka ba ne. Wannan hali na nuna tsoron Allah da gaskiya kuma ya burge ni.”
Ya kuma ƙarfafa jami’in da kada ya karaya saboda ƙin karɓar kuɗin, yana mai cewa abin da ya yi wani babban misali ne da ya kamata a yi koyi da shi.
Otti ya ƙara da cewa zai ci gaba da girmama mutanen kirki kamar Orji, domin su zama abin misali ga sauran al’umma, musamman matasa da ma’aikata.
Laifin da ake zargin bokan da shi
Rahotanni sun nuna cewa a ranar 26 ga Mayu ne aka kama wani boka, Onyeka Obu, wanda aka fi sani da "Ozo Ezeani" bisa zargin birne mutane masu rai.
Lamarin ya faru ne a Umumba Ndiagu, ƙaramar hukumar Ezeagu ta jihar Enugu kuma rundunar ƴan sanda ta jihar Enugu ta ce an cafke wasu mutum uku da ake zargi da haɗin gwiwa da bokan.
Hakazalika, jami’an tsaro sun yi nasarar ceto wata yarinya ‘yar shekara 13 da aka sace domin a yi amfani da ita wajen yin asiri.

Source: Twitter
A gefe guda, Gwamna Otti ya yaba da ƙoƙarin da al’ummar Isiala Ngwa suka yi na shirya taron girmamawa, inda suka tara sama da Naira miliyan 100 domin gudanar da bikin.
An kai farmaki a gidan boka a Enugu
A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda sun kai farmaki gidan wani boka a jihar Eungu da ke Kudancin Najeriya.
Yayin farmakin da aka kai, an yi nasarar cafke wasu mutane da ake zargi suna aiki tare da bokan da yake gidan.
Gwamnatin jihar Enugu ta bayar da umarnin rusa gidan da bokan ya fake da ake zargi yana birne mutane da yin tsafe tsafe a cikinsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

