Babban Kusa a PDP Ya ba Tinubu Shawara kan Kananan Hukumomi

Babban Kusa a PDP Ya ba Tinubu Shawara kan Kananan Hukumomi

  • Tsohon ɗan takarar gwamna na jam'iyyar PDP a jihar Ogun, Segun Showunmi, ya taɓo batun ƴancin gashin kan ƙananan hukumomi
  • Segun Showunmi ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya sanya gwamnoni su aiwatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomin kasar
  • Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa bai kamata Tinubu ya tsaya yana kallon gwamnoni suna ƙananan hukumomi ƴancin cin gashin kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Jigo kuma tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Ogun, Otunba Segun Showunmi, ya ba shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara.

Segun Showunmi ya buƙaci Shugaba Bola Tinubu da ya tilasta wa gwamnoni aiwatar da ƴancin cin gashin kai na kuɗaɗen ƙananan hukumomi.

Segun Showunmi, Bola Tinubu
Segun Showunmi ya ba Tinubu shawara Hoto: Segun Showunmi, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Twitter

Jigon na PDP ya bayyana hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a birnin Abeokuta, babban birnin jihar Ogun, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An yi karar Wike wajen Tinubu kan zargin kashe kudin gwamnati ba bisa tsari ba

Wace shawara aka ba Tinubu kan ƙananan hukumomi?

Ya bayyana gwamnoni a matsayin "yan wasan kwaikwayo" da ke hana aiwatar da ƴancin cin gashin kan ƙananan hukumomi wanda Kotun Ƙoli ta riga ta yanke hukunci a kansa.

"Ban farin ciki da gwamnatin tarayya ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu dangane da yadda suka kai batun zuwa Kotun Ƙoli kan cewa ƙananan hukumomi su riƙa karɓar kuɗinsu kai tsaye da cikakken ƴancin gashin kai."
"Amma sun tsaya sun zauna suna barin wasu ƴan wasan kwaikwayo da suke kiran kansu gwamnoni suna wasa da wannan batu."
“Ina ganin da ya tilasta musu aiwatar da wannan tsarin ƴancin ƙananan hukumomi, ya san yawan ayyukan yi da za a iya samarwa a ƙasar nan?"
"Domin da zarar ƙananan hukumomi sun samu ƴancinsu, za su ɗaukaka matuƙa, kuma akwai hanyoyin da za a iya bi don yin hakan."
“A zamanin Janar Babangida, lokacin yana shugaban ma’aikata na soja, lokacin da suka fara wannan tsarin dimokuraɗiyya, dimokuraɗiyyar NRC da SDP, kun san abin da suka yi?

Kara karanta wannan

Hukumomin EFCC, ICPC sun kwato $967.5bn? Ministan Tinubu ya fayyace gaskiya

"Kuɗin ƙananan hukumomi ba su riƙa bi ta hannun jihohi ba. Suna zuwa ne kai tsaye ma’aikatar kuɗi ta tarayya da ke cikin jihohi domin karɓar kuɗaɗensu. Haka suke yi. Jiha kuma za ta tafi ta karɓi nata daga inda ya dace."

- Segun Showunmi

Segun Showunmi
Segun Showunmi ya yabawa Tinubu Hoto: Segun Showunmi
Source: Twitter

Jigon jam'iyyar PDP ya yabi Bola Tinubu

Jagoran na PDP ya yabawa gwamnatin Tinubu bisa abin da ya bayyana a matsayin "kyakkyawan aiki" da suka yi a cikin shekaru biyu da suka wuce, yana mai cewa sun yi ƙoƙari, rahoton Daily Post ya tabbatar.

Showunmi ya jinjinawa gwamnatin bisa abin da ya kira kyakkyawan tunani wajen warware matsaloli, duk da cewa yana da matsala da wasu manufofi da kuma "salon rayuwa" na wannan gwamnatin.

“A ɓangaren salon rayuwarsu, nan ne nake da matsaloli sosai. Ina da matsaloli da gaske dangane da salon yadda suke gudanar da rayuwarsu."

- Segun Showunmi

Segun Showunmi ya ziyarci Buhari

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Ogun, Segun Showunmi, ya ziyarci Muhammadu Buhari.

Segun Showunmi wanda na hannun daman Atiku Abubakar ne, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasan ne a gidansa da ke Daura.

Jigon na PDP ya bayyana cewa ya yi wa tsohon shugaban ƙasan tambayoyi a yayin tattaunawar da suka yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng