Wike: Musulman Abuja Sun Koka kan 'Katse' Ruwan Famfo a Lokacin Sallar Layya
- Ƙungiyar Abuja Muslim Forum ta roƙi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya dakatar da shirin katse ruwan sha a lokacin bikin Sallah
- Ƙungiyar ta ce katse ruwan na iya janyo matsalolin lafiya musamman yayin bukukuwan babbar sallah da ke bukatar amfani da ruwa sosai
- Wike ya bayyana cewa katsewar na da nasaba da gyaran matatun ruwa guda biyu daga cikin huɗu da ke bai wa birnin na Abuja ruwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ƙungiyar Musulmi a babban birnin tarayya Abuja, wato Abuja Muslim Forum, ta nemi Ministan Abuja, Nyesom Wike, da ya dakatar da shirin da zai janyo katsewar ruwan sha.
Rokon ya zo ne a daidai lokacin da hukumomin FCT suka sanar da wani shiri na haɓaka ayyukan ruwa wanda zai janyo tsaiko na kusan mako biyu.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa kungiyar Musulmai ta ce hakan zai kawo tsaiko a daidai lokacin da Musulmi ke shirin gudanar da bikin Babbar Sallah.
A wata sanarwa da shugaban kungiyar, Alhaji Abdulrazaq Ajani ya fitar, ya bayyana cewa rashin ruwa a irin wannan lokaci na iya zama barazana ga lafiya da walwalar al’umma.
Ruwa: Korafin Musulman Abuja ga Wike
Alhaji Ajani ya bayyana cewa Babbar Sallah lokaci ne da ake amfani da ruwa fiye da kowane lokaci, don haka yin gyaran matatun ruwa da zai janyo tsaiko a lokacin ba daidai ba ne.
Shugaban kungiyar ya ce:
"Muna rokon mai girma Minista Nyesom Wike da ya duba yiwuwar dakatar da wannan shiri na katse ruwan sha a lokacin Sallah...
"Domin kaucewa matsalolin da za su iya tasowa, musamman barazanar barkewar cututtuka."
Ya kara da cewa:
"Ko da yake muna yaba da gyaran da ake shirin yi, amma muna ganin zai fi kyau a dakatar da aikin har sai bayan bukukuwan Sallah domin rage illa ga jama'a."
'Gyaran matatun ruwa ke janyo tsaiko,' Wike
Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa katsewar ruwan na faruwa ne sakamakon gyaran da ake yi wa matatun ruwa guda biyu.
The Nation ta wallafa cewa matatun na daga cikin huɗu da ke bai wa Abuja da garuruwan da ke zagaye da shi ruwa.
Sanarwar da mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Lahadi, ta ce za a yi tsarin raba ruwa na wucin gadi na tsawon mako biyu.

Source: Facebook
Wike ya ce gyaran ya zama dole domin sabunta ingancin ruwan da jama’a ke amfani da shi, tare da tabbatar da tsaron lafiyarsu.
Sai dai hakan ya janwo damuwa daga masu amfani da ruwan, musamman a lokacin da ake buƙatar ruwa sosai a bukukuwan Babbar Sallah.
Wike yana kuka da 'batulcin' gwamna Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce yana kuka idan ya tuna da abin da gwamna Simi Fubara ya masa.

Kara karanta wannan
Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja
Ministan ya yi magana ne domin nuna takaici kan zargin cin amana da tsohon yaronsa, gwamna Fubara ya masa.
Rikicin siyasa tsakanin Fubara da Wike ya yi kamari a jihar Rivers wanda ya kawo sabani mai girma tsakanin 'yan majalisa da gwamnan jihar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

