Bayan Abba Kabir, Gwamna na 2 Ya Rufe Makarantu saboda Shagalin Babbar Sallah
- Bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf, takwaransa na jihar Yobe, Mai Mala Buni ya rufe makarantun gwamnati da na kudi na tsawon kwanaki 10
- Ma'aikatar kula da ilimin firamare da sakandire ta sanar da ba da hutun ne domin bai wa ɗalibai da malamai damar shagalin sallah cikin natsuwa
- A wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar, ta taya ɗaukacin al'ummar musulmi murnar zagayowar idin layya tare da fatan za a yi shagali lami lafiya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni ta bai wa ɗaliban makarantun sakandire da firamare hutun babbar sallah.
Wannan dai na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ba ɗaliban makarantun Kano hutun kwanaki 10 domin su yi shagalin sallah a gida.

Kara karanta wannan
Gwandu: Rikicin dawo da Sarki kan mulki ya zo ƙarshe, Kotun Koli za ta yanke hukunci

Source: Facebook
Sallah: Gwamnatin Yobe ta rufe makarantu
Ma’aikatar Ilimi ta Firamare da Sakandare a Jihar Yobe ce ta sanar da rufe dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu a fadin jihar na tsawon kwanaki 10, rahoton Leadership.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ma'aikatar ta ce an ɗauki wannan matakin ne domin bai wa dalibai da malamai damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin natsuwa kuma tare da iyalansu.
Hakan na kunshe ne a wata sanarwar da Daraktan Kula da Makarantu na Ma'aikatar, Bukar Modu, ya sanyawa hannu a madadin Kwamishinan Ilimi.
Tsawon lokacin da ɗalibai za su shafe a gida
Sanarwar ta bayyana cewa hutun zai fara daga ranar Laraba, 4 ga Yuni, 2025, zuwa Lahadi, 15 ga Yuni, 2025.
Rufe makarantun ya zo dai-dai da sanarwar fadar sarkin musulmi, wadda ta nuna cewa a ranar Juma’a, 7 ga Yuni, a matsayin ranar Babbar Sallah (Eid-el-Kabir).
Haka zalika, bayan sallah, akwai kuma bukin Ranar Dimokuradiyya wanda za a yi a ranar Laraba, 12 ga Yuni, 2025.

Kara karanta wannan
Akpabio: Sanata Natasha ta saki sabon bidiyo kan yadda ake 'wawure kuɗi' a Majalisa

Source: Original
Dalilin rufe makarantun gwamnati a Yobe
Ma’aikatar ta bukaci dukkan makarantun gwamnati a faɗin jihar Yobe da masu zaman kansu su ba da hutu na tsawon wannan lokaci domin bai wa dalibai, malamai da sauran masu ruwa da tsaki damar yin sallah cikin walwala.
Kwamishinan Ilimi na jihar Yobe, Farfesa Adam Idris, ya mika sakon fatan alheri da murna ga daukacin al’ummar Musulmi bisa zagayowar wannan lokaci mai daraja.
Ya kuma bukaci iyaye da su sanya ido sosai kan harkokin ‘ya’yansu a lokacin da bayan bikin domin tabbatar da tsaro da tarbiyya, tare da yi musu fatan alheri a wannan lokaci mai albarka.
Gwamnatin Tinubu ta ba da hutun sallah
A wani labarin, kum ji cewa gwamnatin tarayya ta ayyana Juma’a, 6 da Litinin, 9 ga Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutun babba sallah ta bana.
Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da aka fitar ranar Litinin, 2 ga watan Mayu, 2024.
Dr. Tunji-Ojo ya taya dukkan al’ummar Musulmi, a gida Najeriya da ma na kasashen waje, murnar zagayowar wannan babbar rana ta Sallah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng