Malamin Addini Ya Yabi Tinubu, Ya Fadi inda Ya Kerewa Buhari

Malamin Addini Ya Yabi Tinubu, Ya Fadi inda Ya Kerewa Buhari

  • Primate Elijah Ayodele ya kwararo yabo ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu yayin da ya cika shekara biyu mulki
  • Malamin addinin na Kirista ya bayyana cewa Tinubu ya fi Muhammadu Buhari ƙoƙari a cikin shekara biyu da ya yi a mulki
  • Sai dai, duk da haka ya bayyana cewa akwai wuraren da shugaban ƙasa ya kamata ya ƙara maida hankali a kansu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban cocin INRI Evangelical Spiritual Church, Primate Elijah Ayodele, ya yabawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Primate Ayodele ya yabawa Shugaba Tinubu ne bisa nasarorin da ya cimma cikin shekaru biyun farko a mulkinsa.

Primate Ayodele, Bola Tinubu
Primate Ayodele ya ce Tinubu ya fi Buhari Hoto: Primate Elijah Ayodele, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Osho Oluwatosin, ya sanya wa hannu, cewar rahoton jaridar Tribune.

Primate Ayodele ya fifita Tinubu kan Buhari

Kara karanta wannan

"Ya gaza": Tsohon gwamna ya caccaki Tinubu kan kuntatawa 'yan Najeriya

Primate Ayodele ya bayyana cewa Tinubu ya fi tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ƙoƙari a cikin shekaru biyun farko na mulkinsa, musamman a ɓangaren tattalin arziƙi, kayan abinci, rashin tsaro, da ababen more rayuwa.

Sai dai ya kuma jaddada cewa akwai wasu fannoni da bai yi ƙoƙari sosai ba, kuma ya kamata a gyara.

“Abin da nake gani a yanzu shi ne zai kasance lokaci mai matukar ƙalubale ga shugaban ƙasa. Ya fi Buhari ƙoƙari a fannin tattalin arziki, kayan abinci, makamashi, rashin tsaro da kuma ababen more rayuwa."
"Duk da haka, akwai wasu ɓangarori da bai taɓuka abin a zo-a gani ba, musamman fannin taimakawa matasa."
“Ayyukan manyan titunan da yake yi su na da matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziƙin ƙasar nan. Idan wani ɗan adawa ne kan kujerar, wataƙila da bai samu irin wannan ci gaba da Tinubu ya samu ba a cikin shekaru biyu."

- Primate Elijah Ayodele

Malamin addini ya ba Tinubu shawara

Yayin da yake ƙarin bayani kan abin da ya kamata shugaban ƙasa ya mayar da hankali a kai, Primate Ayodele ya buƙace shi da ya yi aiki tuƙuru wajen samar da ayyukan yi ga matasa da kuma karfafa haɗin kan ƙasa.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya fito karara ya gayawa Tinubu abin da zai hana shi tazarce a 2207

Primate Ayodele
Primate Ayodele ya yabawa Shugaba Tinubu Hoto: Primate Elijah Ayodele
Source: Twitter

Primate Ayodele ya kuma shawarce shi da ya rage wahalar da ake fama da ita, ta hanyar sauƙaƙa farashin kayan abinci a cikin ƙasar nan.

Ya gargaɗe shi da kada ya bar manufofi marasa kyau su ɓata irin nasarorin da ya samu, tare da buƙatar a cire ministocin da ba sa aiki yadda ya kamata daga cikin majalisar zartarwa.

Ƙungiyar Afenifere ta caccaki Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar Yarbawa ta Afenifere ta bayyana cewa shugaban ƙasa Bola Tinubu ya jefa ƴan Najeriya cikin halin ƙunci.

Ƙungiyar ta bayyana cewa manufofin da gwamnatin Tinubu ta kawo sun gaza samar da ci gaban da aka ce za su samar a ƙasar nan.

Ta nuna cewa gwamnatin Tinubu babu abin da ta fi maida hankali a kai face yaɗa bayanan ƙarya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng