Bayan Tsokano Manya a Abuja, Wike Ya Fadi Abin da Yake Sanya Shi Farin ciki
- Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya nuna cewa yana jin daɗin taka manyan mutane da suke ganin sun fi ƙarfin doka
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa babu ɗaga ƙafa kan batun biyan kuɗin harajin fili da ake bin masu kadarori bashi a birnin Abuja
- Ya zargi waɗanda suƙa gabace shi a kujerar, da gaza yin abin da ya dace wajen tabbatar da cewa an biya kuɗaɗen wadannan filaye
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya yi magana kan biyan kuɗin harajin fili.
A matsayin da yake kai tun a watan Agustan 2023, Nyesom Wike ya bayyana cewa yana jin daɗin taka manyan mutane.

Source: Facebook
Wike ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a Abuja, ranar Litinin, cewar rahoton tashar Channels tv.

Kara karanta wannan
Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Nyesom Wike ya ja kunnen masu kadarori a Abuja
Ministan ya ce duk masu kadarori a Abuja da ba su biya kuɗin harajin filinsu ba, dole ne su biya, ko kuma su fuskanci hukunci, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya soki wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP ciki har da Bode George, inda ya ce dole ne PDP ta biya kuɗin harajin filin da sakatariyar jam’iyyar ke kai a Abuja.
Wike ya ce waɗanda suka gabace shi a kujerar ministan Abuja, ciki har da gwamnan jihar Bauchi na yanzu, Bala Mohammed, ba su da ƙarfin halin yin abin da ya dace.
Ministan ya ce sun gaza tilasta wa manyan ƴan siyasa masu kadarori a babban birnin ƙasar nan su biya harajin filin su na shekara-shekara.

Source: Facebook
Wike ya ce yana jin daɗin taka manya
“Dubi abin da muke yi da ya bambanta. Mutane suna cewa babu wani aiki a FCT, amma yanzu ana gani, wanda hakan ke nuna cewa ina aiwatar da abubuwan da su tsofaffin ministocin suka kasa yi."
"Na gano cewa mafi yawan su ba su da ƙarfin hali su ɓata wa mutane rai, su taka su. Amma ni ina jin daɗi idan na taka manyan mutane, waɗanda ke cewa ‘ba za a iya yi mana komai ba’, amma ni na ce za a yi. Wannan shi ke faranta min rai."
“Abin da suke so na yi shi ne na ɗauki matakai kan talakawa, su ce ‘ba za a yi wa masu kuɗi komai ba’, amma ni na ce za a yi musu. Wannan ne ya sa muke samun sakamako. Idan ba ka yi abin da ya dace ba, to wannan laifinka ne. Ni ba ruwana."
- Nyesom Wike
Ministan Abuja ya faɗi matsalar da yake fuskanta
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana matsalar da yake fuskanta a muƙaminsa.
Wike ya bayyana cewa babbar matsalar da yake fuskanta a kujerar minista, ita ce ƙin biyan haraji da mazauna Abuja suke yi.
Ministan ya koka da cewa jama'a na son su ga ana aiwatar da muhimman ayyukan ababen more rayuwa, amma ba su damu da inda gwamnati za ta samo kuɗaɗen ba.
Asali: Legit.ng
