Ambaliya: Buhari Ya Girgiza da Mutuwar Mutane Kusan 200 a Kano da Neja

Ambaliya: Buhari Ya Girgiza da Mutuwar Mutane Kusan 200 a Kano da Neja

  • Tsohon Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya bayyana alhininsa kan mutuwar mutane fiye da 100 sakamakon ambaliya a Neja
  • Muhammadu Buhari ya kuma mika sakon ta’aziyya kan hadarin mota da ya hallaka ‘yan wasa da jagororinsu 22 a jihar Kano
  • Ya bayyana cewa aukuwar wadannan abubuwa a lokaci guda ya girgiza shi matuka, yana fatan wadanda suka jikkata za su warke da wuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari, ya aike da sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu a ambaliyar ruwa da kuma hadarin mota da suka auku a Kano da Neja.

Ambaliyar da ta afku a jihar Neja ta hallaka sama da mutum 100 tare da rusa gidaje da dama da kuma raba dubban mutane da muhallansu.

Kara karanta wannan

Fitattun ƴan wasan Kano 21 sun mutu a hanyar komawa gida daga jihar Ogun

Buhari
Buhari ya yi jaje bayan hadura a Kano da Neja. Hoto: Garba Muhammad
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanan da Muhammadu Buhari ya yi ne a cikin wani sako da aka wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bangare guda kuma, mutum 22 da suka hada da matasa ‘yan wasa, masu horarwa da jami’an kwamitin wasanni, sun rasu a wani mummunan hadarin mota a jihar Kano.

A wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu, ya fitar ranar 1 ga Yuni, Buhari ya bayyana cewa wadannan abubuwan sun girgiza shi kwarai da gaske.

Buhari ya yi wa jihohin Neja da Kano jaje

Buhari ya bayyana cewa haduran da suka auku cikin dan kankanin lokaci sun girgiza shi da kuma da dama daga cikin ‘yan Najeriya da ma sauran mutane a duniya.

A cewarsa, rashin da aka samu sakamakon wadannan bala’o’i na daga cikin abubuwan da ke jefa al’umma cikin damuwa da bakin ciki.

Shugaba Buhari ya ce:

“Zuciyata ta kadu saboda mutuwar da aka samu sakamakon ambaliya a jihar Neja da hadarin mota a Kano. Wannan lamari abin takaici ne matuka,”

Kara karanta wannan

Magidanci ya kidime, ya suma bayan matarsa ta haifi 'yan 3 a asibitin Kogi

Ya kara da cewa yana mika ta’aziyyarsa ga dukkan iyalan da suka rasa ‘yan uwa, abokai da makusanta, tare da fatan Allah ya ba su hakuri da juriya.

Shugaba Buhari ya kuma roki Allah ya ba wa wadanda suka jikkata cikakken sauki cikin gaggawa.

Ambaliya
Ambaliya ta kashe mutane sama da 100 a Neja. Hoto: Yax Mokwa
Source: Facebook

Buhari ya karfafi mutanen Kano da Neja

Tsohon shugaban ya bayyana cewa yana tare da gwamnatocin jihohin Neja da Kano da kuma daukacin al’ummar yankunan da abin ya shafa a wannan lokaci na bakin ciki.

Muhammadu Buhari ya kuma yi addu’a da fatan irin wadannan abubuwa kada su sake aukuwa a gaba.

Tuni dai hukumomi da kungiyoyin agaji suka fara kai dauki ga wadanda abin ya shafa a Neja, yayin da hukumomin Kano su ka ba da hutu saboda aukuwar hadarin motar.

Gwamnoni sun yi magana kan ambaliyar Neja

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnonin Najeriya sun yi ta'aziyya ga mutanen jihar Neja bayan ambaliyar ruwa a Mokwa.

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutane 150 ne suka rasa rayukansu saboda ambaliyar ruwan da ta auku a jihar.

Kungiyar gwamnonin Najeriya ta yaba da matakin da gwamnan jihar, Umaru Bago ya dauka bayan ambaliyar ruwan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng