Akpabio Ya ba Gwamnoni Mafita kan Zabar Wadanda Za Su Gaje Su

Akpabio Ya ba Gwamnoni Mafita kan Zabar Wadanda Za Su Gaje Su

  • Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi kira da babbar murya ga gwamnonin da ke kan wa'adi na biyu na mulki
  • Godswill Akpabio ya buƙaci gwamnonin da su tsaya su yi karatun ta natsu wajen zaɓar mutanen da za su gaje su
  • Tsohon gwamnan na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa kuskure wajen zaɓar waɗanda za suɓagje su ke sanyawa ana samun cin amana

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Legas - Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya shawarci gwamnonin da ke wa’adin mulki na biyu da su yi taka-tsantsan wajen zaɓar waɗanda za su gaje su.

Godswill Akpabio ya gargaɗi gwamnonin game da miƙa mulki ga mabiyan da ba su da wani shiri ko ƙwarewa.

Godswill Akpabio
Akpabio ya ba gwamnoni shawara Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya bayar da wannan shawara ne a ranar Asabar, yayin ƙaddamar da sashen farko mai tsawon kilomita 30 na titin gabar teku daga Legas zuwa Calabar, a yankin Lekki, jihar Legas, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron ya samu halartar shugaban ƙasa Bola Tinubu, fitaccen marubuci, Wole Soyinka, ministan kuɗi, Wale Edun, ministan ayyuka, Dave Umahi, gwamnan Imo, Hope Uzodimma, gwamnan Ogun, Dapo Abiodun da gwamnan Legas, Babajide Sanwo-Olu da wasu manyan baƙi.

A cewar Akpabio, wanda shi ma tsohon gwamna ne na jihar Akwa Ibom, dole ne gwamnonin da za su bar mulki su kauce wa baragurbi a matsayin waɗanda za su gaje su, rahoton tashar Channels tv ya tabbatar.

Akpabio ya jaddada cewa irin hakan ne ke kai ga cin amana da rushewar dangantaka bayan sun bar ofis.

Wacce shawara Akpabio ya ba gwamnoni?

"Muna da shugaban ƙasa da ke da hangen nesa da gani mai zurfi. Wannan ya sa nake ganin ya dace na ba da wata shawara ga gwamnonin da ke wa’adin su na biyu."
"Kada ku miƙa mulki ga wanda bai nemi mulki ba. Kada ka ba wa wanda bai shirya ba."

Kara karanta wannan

"Shugabanci akwai wahala," Gwamna ya roki malamai su riƙa gaya masu gaskiya

"Kada ka ɗauka a zuciyarka cewa wannan yaro yana da ladabi, kullum yana durƙusa idan yana magana da kai, matarsa kuwa kullum tana ɗuƙawa ƙasa. Sai ka ce, bari na ɗora wannan a kan mulki."
"Idan ka yi haka, kana miƙa mulki ne ga wanda bai shirya ba, kuma hakan zai kai ga ya ba ka kunya. Wannan ne inda cin amana ke farawa. Ina ƙoƙarin ba da shawara ne kawai."
"Ga gwamnonin APC, ina da tabbacin cewa kuna ƙoƙari saboda kuna da jagora wanda ke da hangen nesa."

- Godswill Akpabio

Godswill Akpabio
Akpabio ya bukaci gwamnoni su yi taka tsan-tsan Hoto: Godswill Obot Akpabio
Source: Facebook

Akpabio ya ba Peter Obi shawara

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya caccaki Peter Obi, kan wasu kalamai da ya yi.

Godswill Akpabio ya buƙaci Peter Obi da ya tsaya ya warware matsalolin da suka addabi jam'iyyarsa ta LP, wacce ya yi takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashinta.

Akpabio ya bayyana cewa idan har Peter Obi ba zai iya kawo ƙarshen matsalolin LP ba, to bai cancanci ya mulki ƙasa kamar Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng