Gwamna Abba Ya Ayyana Ranar Hutu don Jimamin 'Yan Wasan da Suka Rasu

Gwamna Abba Ya Ayyana Ranar Hutu don Jimamin 'Yan Wasan da Suka Rasu

  • Gwamnatin jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta nuna alhininta kan hatsarin da ya yi sanadiyyar rasuwar wasu ƴan wasa
  • A bisa hakan ne sai Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ayyana ranar Litinin, 2 ga watan Yunin 2025 a matsayin ranar hutu don jimamin rashin da aka yi
  • Gwamnan ya buƙaci jama'ar jihar da su yi amfani da lokacin wajen sanya mamatan tare da iyalansu cikin addu'o'insu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ayyana Litinin, 2 ga Yunin 2025 a matsayin ranar hutu na musamman.

Gwamna Abba ya ba da hutun ne domin jajantawa iyalan waɗanda suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsarin mota da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 22 tare da raunata wasu da dama.

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya ayyana ranar hutu a Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Bikin Sallalh: Gwamna Ahmed Aliyu ya gwangwaje ma'aikatan jihar Sokoto

Abba Kabir Yusuf ya ba da umarnin ne duk da cewa yana cikin Aikin Hajji na 2025 a Saudiyya.

Gwamnan ya nuna alhininsa tare da miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Waɗanda hatsarin ya rutsa da su yawancinsu matasa ne, waɗanda ke kan hanyarsu ta komawa gida bayan wakiltar Kano a gasar wasanni ta ƙasa.

Gwamnatin Kano ta ba da hutu

A cikin sanarwar gwamnatin jihar ta ayyana ranar Litinin a matsayin ranar hutu don jajantawa iyalan mamatan.

Sanarwar ta ce tawagar ta ƙunshi ƴan wasa, masu horarwa da jami’an gwamnati, waɗanda suka wakilci jihar a wasannin da suka kammala kwanan nan.

"A madadin gwamnatin jihar Kano da al’ummar jihar, muna miƙa ta’aziyyar mu bisa wannan babban rashi da ya auku ga jaruman ƴan wasan Kano a hanyarsu ta komawa gida a kan hanyar Kano-Zariya."
"Da zuciya mai cike da baƙin ciki ne na karɓi labarin wannan hatsari mai ban tausayi, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan kasa 22 masu daraja tare da raunata wasu da dama."

Kara karanta wannan

Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja

"A madadin gwamnati da al’ummar Kano, muna miƙa ta’aziyyar mu ga iyalan mamatan. Muna alhini tare da ku, kuma muna cikin wannan jimami tare da ku."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamna Abba ya yi alhinin rasuwar 'yan wasan Kano Hoto: Abba Kabir Yusuf
Source: Facebook

Gwamna Abba ya buƙaci a yi musu addu'a

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan lamarin a matsayin lokaci mai wahala ga jihar Kano gaba ɗaya, tare da kiran jama’a da su kasance cikin natsuwa da haɗin kai.

Ya kuma tabbatar da cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin tallafa wa waɗanda abin ya shafa da iyalansu.

Har ila yau, gwamnatin jihar ta buƙaci dukkan limamai da Musulmi a ciki da wajen Kano da su yi addu’ar neman gafara ga waɗanda suka rasa rayukansu da iyalansu domin jure wannan rashin da suka yi.

Gwamna Abba ya biya kansilolin Ganduje haƙƙoƙinsu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya fara biyan bashin kuɗaɗen sallama da kansilolin da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta hana kuɗaɗensu.

Waɗanda suka ci gajiyar biyan bashin sun haɗa da kansiloli daga shekarar 2014 zuwa 2015 na ƙananan hukumomi 44 da ke jihar.

Gwamna Abba ya bayyana cewa biyan kansilolin haƙƙoƙinsu ba wata alfarma ba ce, illa kawai an yi abin da ya dace ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng