Ambaliya: Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Mutuwar Mutane Sama da 100 a Jihar Neja
- Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi alhinin ambaliyar ruwan da ta faru a Mokwa ta jihar Neja ranar Alhamis
- Pantami ya miƙa sakon jaje ga waɗanda lamarin ya shafa, tare da kira ga gwamnatin tarayya da jihohi su kai wa mutane agaji
- Hukumomi a jihar Neja sun tabbatar da cewa an gano gawarwakin mutane aƙalla 115 da ambaliyar ruwan ta yi ajalinsu, wasu da dama sun ɓata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Niger - Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Sheikh Isa Ali Pantami ya yi alhinin ambaliyar ruwan da ta afku a garin Mokwa na jihar Neja.
Farfesa Pantami ya miƙa sakon jaje ga duka mazauna garin Mokwa, hedikwatar karamar hukumar Mokwa, tare da addu'ar Allah Ya jiƙan waɗanda suka rasu.

Source: Facebook
Tsohon ministan ya miƙa wannan saƙo ne a wata gajeruwar sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook da safiyar yau Asabar, 31 ga watan Mayu, 2024.

Kara karanta wannan
Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya
Idan baku manta ba a ranar Alhamis da ta shuɗe aka yi ambaliyar ruwa a kauyukan Tiffin Maza da Anguwan Hausawa sakamakon mamakon ruwan da aka yi a daren Laraba.
Sama da mutane 115 sun mutu a Neja
Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa ambaliyar ruwan ta tafka ɓarna a yankin ƙaramar hukumar Mokwa, inda ta rusa gidaje tare ɓarnata dukiyoyi masu ɗumbin yawa.
Hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Neja (NSEMA) ta bayyana cewa tawagar da ke aikin ceto ta gano gawarwakin mutane 115 zuwa ƙarfe 5:00 na yammacin jiya Juma'a.
Daraktan NSEMA, Abdullahi Baba Arah, ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai, ta bakin jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Hussain.
Pantami ya buƙaci gwamnatoci su agaza wa mutane
Da yake magana kan lamarin, Malam Pantami ya buƙaci gwamnatin tarayya, gwamnatocin jihohi da kamfanoni su taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa.

Kara karanta wannan
Ambaliyar Neja: Babban masallaci ya rufta kan Musulmai, sama da mutum 100 sun rasu

Source: Facebook
"Muna mika jaje zuwa ga yan'uwanmu mutanen Mokwa da ke Jihar Neja a Najeriya dalilin ambaliyar ruwa da ya yi sanadiyyar rasuwar mutane sama da 110 da kuma lalacewar gidaje sama da 3,000 kamar yadda rahoto ya nuna."
"Bil hakika wannan babban jarrabawa ne, gare mu gaba daya. Muna kira da babbar murya ga gwamnatin tarayya da sauran kamfanoni da gwamnatocin jihohi da su taimakawa wadannan bayin Allah.
"Muna kara addu'ar Allah Ya kiyaye faruwansa nan gaba. Allah Ya karbi wadanda suka rasu a matsayin shahidai, Ya kyautata na mu bayan na su."
- Farfesa Isa Pantami.
Mokwa: Mutum 12 yan gida ɗaya sun mutu
A wani rahoton, mun kawo cewa mutane 12 ƴan gida daya sun mutu a ambaliyar ruwan da ta afku a akuyuka biyu a karamar hukumar Mokwa, jihar Neja.
Rahotanni sun bayyana cewa ambaliyar da aka ce ta samo asali ne daga ruwan sama mai karfi da aka yi a daren Laraba, ta fi shafar yara da mata.
wata mata a yankin, Hajiya Hassana Mokwa, ta ce mutane 12 daga cikin iyalanta su 13 sun mutu a ambaliyar, yayin da daya kacal ya tsira kuma yana asibiti.
Asali: Legit.ng