Hukumomin EFCC, ICPC Sun Kwato $967.5bn? Ministan Tinubu Ya Fayyace Gaskiya
- Antoni Janar na tarayya kuma ministan shari'a, Lateef Fagbemi, ya yi magana kan rahotannin da ke cewa EFCC, ICPC sun ƙwato $967.5bn
- Lateef Fagbemi ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiga a cikin rahotannin waɗanda aka yi ta yayatawa
- Ministan shari'an ya bayyana cewa adadin abin da hukumomin yaƙi da cin hancin suka ƙwato a shekarar 2024 bai kai hakan ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Antoni Janar na tarayya kuma ministan Shari'a, Lateef Fagbemi, ya ƙaryata ikirarin cewa gwamnatin tarayya ta ƙwato dala biliyan $967.5bn daga hannun ɓarayin dukiyar ƙasa.
Lateef Fagbemi ya bayyana cewa sam ba haka ba ne adadin kuɗaɗen da hukumomin EFCC da ICPC suka ƙwato.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta ce ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a taro kan ƙwato dukiya da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.

Kara karanta wannan
Kudin mazaɓa: Tinubu ya ba kowane ɗan Majalisar Tarayya Naira biliyan 1? Bayanai sun fito
Ya bayyana cewa ainihin adadin da aka ƙwato bai kai hakan ba, duk da cewa har yanzu yana da matuƙar muhimmanci, rahoton jaridar Tribune ya tabbatar.
Fagbemi ya musanta ƙwato $967.5m
Fagbemi ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka fitar ranar Juma'a.
"Saɓanin abin da ake yayatawa, adadin abin da aka ƙwato shi ne dala miliyan $105.9, ba dala biliyan $967.5 ba."
"A shekarar 2024 kaɗai, hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) ta ƙwato fiye da Naira biliyan 248, dala miliyan $105, da kuma gidaje guda 753."
"Hukumar ICPC ma ta ƙwato tsabar kuɗi Nira biliyan 29.685 da kuma kadarar da ta kai dala $966,900."
- Lateef Fagbemi
Ya ce daga shekarar 2017 zuwa yanzu, Najeriya ta yi aiki tare da abokan hulɗarta na ƙasashen waje inda aka ƙwato kusan dala miliyan $763.7 da kuma fam £6.47 miliyan.
Ya ce cikin wannan adadin, a shekarar 2024 kaɗai, an ƙwato kusan dala $102.88 miliyan da kuma fam £2.06 miliyan.
Fagbemi ya yi kira ga gidajen jaridu da suka buga adadi na dala biliyan $967.5 da su gyara rahotanninsu, yana mai cewa:
"Adadin da marubutan suka ambata ba daidai ba ne, kuma ya sha bamban da bayanan da na gabatar."

Source: Facebook
Gwamnati na amfani da kuɗaɗen da aka ƙwato
Ya yaba da matakin gaskiya da nuna adalci da gwamnatin tarayya ke ɗauka, yana mai cewa ana amfani da kuɗaɗen da aka ƙwato wajen aiwatar da manyan ayyuka.
"Daga 2017 zuwa 2024, an yi amfani da waɗannan kuɗaɗen wajen gina muhimman hanyoyi kamar titin Lagos-Ibadan, Gada ta biyu ta Kogin Naija, da hanyar Abuja zuwa Kano."
- Lateef Fagbemi
Ya ƙara da cewa kuɗaɗen da aka ƙwato na kuma taimakawa wajen haɓaka kiwon lafiya, ayyukan samar da makamashi, da kuma fannin shari’a a ƙasar nan.
Eno ya magantu kan zuwa EFCC
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya yi magana kan faɗawa komar EFCC bayan ya sauka daga mulki.
Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa ba za a riƙa ganinsa wajen hukumar EFCC bayan ya gama wa'adinsa na mulki.
Umo Eno ya nuna cewa ba zai bari buƙatun jama'a su tilasta masa karkatar da kuɗaɗen gwamnati ba.
Asali: Legit.ng

