Magidanci Ya Kidime, Ya Suma bayan Matarsa Ta Haifi 'Yan 3 a Asibitin Kogi

Magidanci Ya Kidime, Ya Suma bayan Matarsa Ta Haifi 'Yan 3 a Asibitin Kogi

  • Wani mutum mai suna Adamu Muhammed ya suma a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lokoja bayan jin cewa matarsa ta haifi ‘yan uku
  • An ceto mutumin da gaggawa bayan ya fadi sumamme saboda kaduwa da rashin shiri wajen kula da jariran guda uku da aka haifa
  • Rahoto ya nuna cewa iyalan mutumin na neman taimako daga gwamnati da masu hannu da shuni domin kula da jarirai da biyan kudin asibiti

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kogi - Wani lamari mai ban tausayi ya faru a asibitin koyarwa na jami’ar tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi, yayin da wani mutum ya suma bayan jin cewa matarsa ta haifi ‘yan uku.

Mutumin, mai suna Adamu Muhammed Tenimu, ya ce bai taba tsammanin matarsa za ta haifi yara uku a lokaci guda ba, duka mata, lamarin da ya gigita shi kwarai.

Kara karanta wannan

Matashi ya saya wa Tinubu ragon layya, ya yi wa mamar shugaban kasa mai suna

Federal Teaching Hospital Lokoja
Magidanci ya suma bayan matarsa ta haifi 'yan 3 a Kogi. Hoto: Federal Teaching Hospital Lokoja
Source: Facebook

Rahoton jaridar Punch ya nuna cewa an gaggauta kai masa agaji domin ceto shi, yayin da uwar da jariran suke cikin koshin lafiya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Miji ya suma bayan matarsa ta haifi 'yan 3

Bayan haihuwar, da aka tabbatar cewa an samu nasara ba tare da matsala ba, Adamu ya samu labarin cewa an haifi ‘yan uku, inda nan take ya gigice ya fadi.

Wanda lamarin ya faru a gabansa ya bayyana cewa Adamu bai da wata matsala ta lafiya, sai dai ya kasa jure girman nauyin da ke gabansa ne kawai.

Jami’an asibiti da wasu da ke wajen ne suka taimaka suka farfado da shi, inda daga bisani ya bayyana jin daɗi da kuma damuwar da ke zuciyarsa.

"Bamu da shirin ɗaukar nauyin su" – Adamu

Da yake magana da manema labarai, Adamu ya bayyana cewa su dai sun shirya ne da niyyar karbar jariri guda daya, ba uku ba.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

Ya ce rashin kudi ya hana su yin gwajin yau da kullum da zai iya nuna cewa 'yan uku ne cikin, kuma yanzu ba su da isasshen kudi domin biyan kudin asibiti ko sayen kayan jarirai.

Mijin matar ya ce:

“Na gode wa Allah da wannan baiwa, amma gaskiya ina cikin rudani. Bamu shirya ba, kuma bani da ko kobo da zan saya musu kayan da ake bukata.”

An fara kira da a tallafa wa iyalin mutumin

‘Yan uwa da abokan arziki sun fara neman taimako daga gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu domin tallafa wa iyalan mutumin.

Wani makusancisa, Nuhu Alhassan, ya ce:

“Adamu mutum ne mai halin kirki da gaskiya. Wannan lamari na bukatar kulawa ta musamman daga hukumomi da mutane masu hannu da shuni.”
Ododo
An bukaci gwamnatin Kogi ta tallafawa mutumin da matarsa ta haifi 'yan 3. Hoto: Kogi State Government
Source: Facebook

An kuma roki Ma’aikatar Kula da Harkokin Mata da Cigaban Al’umma ta jihar Kogi da ta sa hannu wajen taimaka wa mutumin.

An sace jariri a gidan suna a Nasarawa

A wani rahoton, kun ji cewa an kama wata mata da zargin sace jariri a gidan suna a jihar Nasara da ke Arewa ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Ambaliya: Ana tsoron rayuka sama da 50 sun salwanta bayan gano gawarwaki 15 a Neja

Rahotanni sun nuna cewa matar da ake zargi da satar da shiga gidan suna ne bayan haihuwa, ta fara kokarin sace yaron da aka haifa.

Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta tabbatar da kama matar tare da tabbatar da cewa za a yi bincike domin hukunta mai laifi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng