Faransa Ta Raba Tallafin Kusan Naira Biliyan 2 a Najeriya

Faransa Ta Raba Tallafin Kusan Naira Biliyan 2 a Najeriya

  • Gwamnatin Faransa ta bayar da tallafin Naira biliyan 1.8 ga kungiyoyi 19 a Najeriya domin taimakawa al'umma
  • An bayyana cewa kudin tallafin na cikin wani shiri ne da ke da nufin magance matsalolin wariyar jinsi, talauci da rikice-rikice a al’umma
  • Ofishin jakadancin Faransa ya ce ba za ta tilasta wata ajanda daga ƙasarta ga Najeriya ba, sai dai taimakawa ƙarfafa cigaba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Gwamnatin Faransa ta bayar da tallafin kudi har €1m, daidai da Naira biliyan 1.8, ga kungiyoyi 19 na farar hula (CSOs) a sassa daban-daban na Najeriya.

An bayyana cewa tallafin na karkashin shirin FEF-OSC da ofishin jakadancin Faransa ke aiwatarwa a Najeriya.

Faransa
Faransa ta raba tallafin N18bn a Najeriya. Hoto: @GRA_Nigeria
Source: Twitter

Legit ta tattaro bayanin ne a wani sako da ofishin jakadancin Faransa ya wallafa a X bayan kammala taron raba tallafin a Abuja.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: An sanya ranar fara sabuwar zanga zangar adawa da mulkin Tinubu

A kan me tallafin Faransa zai mayar da hankali?

Rahoton the jaridar the Guardian ya nuna cewa jakadan Faransa a Najeriya, Bertrand de Seissan ya yi karin haske game da tallafin.

Bertrand de Seissan ya bayyana cewa za a mai da hankali ne kan rage cin zarafin mata da tallafawa matasa da masu rauni ta hanyar samar musu da hanyar dogaro da kai.

Ya kara da cewa kowace kungiya daga cikin 19 da aka zaɓa ta samu tallafin shekara guda bayan tsauraran matakai na tantancewa don tabbatar da inganci da tasirin shirin.

'Ba za mu kakaba ajandar waje ba' – Faransa

Ofishin jakadancin Faransa ya bayyana a fili cewa wannan shiri ba wata hanya bace ta tilasta ajandar wata kasa kan Najeriya, sai dai taimako ne na goyon bayan cigaban jama'a.

Bertrand ya ce:

“A cikin wannan shiri akwai mutane – mata, maza da matasa – da ayyukan kungiyoyin Najeriya za su canza musu rayuwa."

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

Faransa
Faransa ta ce ba za ta kakaka wata ajanda a Najeriya ba. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Faransa za a inganta kwarewar kungiyoyi

Jami’ar haɗin gwiwa a ofishin jakadancin Faransa, Ketty Regis ta ce ana aiki tare da Ma’aikatar Harkokin Mata domin tabbatar da dorewar shirin.

Ta ce shirin na daya daga cikin matakan diplomasiyyar mata ta Faransa, wanda ke kokarin tabbatar da daidaito da damar ci gaba ga kowa cikin al’umma.

Tasirin taimako Faransa a Najeriya

Ketty ta kuma jaddada cewa an fara ayyukan ne sakamakon haɗin gwiwa tsakanin Faransa da Najeriya wajen karfafa juna a matakin gwamnati da na al’umma.

Shirin zai kuma bai wa kungiyoyin fararen hula horo a fannonin dabarun aiki, tsare shirye shirye da sauransu.

Wata kungiyar bincike a Najeriya da ta samu shiga shirin ta wallafa sakon godiya ga ofishin jakadancin Faransa a shafinta na X.

Faransa za ta horas da jami'an NDLEA

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin Faransa ta fara cika alkawarin da ta kulla da shugaban Najeriya, Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Bayanin da Bola Tinubu ya yi wa Najeriya bayan cika shekara 2 a kan mulki

Gwamnatin Faransa ta yi alkawarin aiki da Hukumar NDLEA ta Najeriya wajen ba jami'anta horo na musamman.

Shugaban hukumar NDLEA, Janar Buba Marwa (Mai ritaya) ya yaba da kokarin kasar Faransa na hada karfi da karfe da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng