Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Kasa kan Boko Haram, an Kashe Mayaka 60

Sojoji Sun Yi Luguden Wuta Ta Sama da Kasa kan Boko Haram, an Kashe Mayaka 60

  • Sojojin Operation Hadin Kai sun kashe aƙalla ‘yan ta’adda 60 a wani gagarumin artabu da suka yi da Boko Haram a Bita, jihar Borno
  • Harin ya faru ne da tsakar dare a ranar Juma’a, inda sojoji suka samu taimakon jiragen yaki wajen ragargazar mayakan ISWAP
  • Jami’an tsaro sun bayyana cewa farmakin na daga cikin mafi tasiri da nasara da suka taba samu a baya-bayan nan kan Boko Haram

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Borno - Sojojin Najeriya da ke ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kashe aƙalla ‘yan ta’adda 60 a wani gagarumin farmaki da suka kai wa Boko Haram a garin Bita da ke jihar Borno.

Rahotanni sun tabbatar da cewa farmakin na cikin manyan nasarorin da sojojin Najeriya suka samu kan 'yan ta'adda a 'yan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sace mutane sama da 100 bayan kai mummunan hari Kebbi

Sojoji
Sojoji sun kashe Boko Haram 60 a Borno. Hoto: Nigeria Air Force
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan farmakin da sojojin da suka kai ne a cikin wani sako da rundunar sojin Najeriya ta wallafa a X.

Rahoto ya nuna cewa farmakin ya haɗa da hare-haren ƙasa da na sama, kuma an gudanar da shi da tsakar dare, wanda ya janyo mummunan hasara ga ‘yan ta’addan.

Wannan farmaki na zuwa ne a daidai lokacin da dakarun Najeriya ke ci gaba da fafutukar murkushe mayaƙan ISWAP a yankunan Arewa maso Gabas.

An kashe mayakan Boko Haram 60 a Borno

Rahotanni sun ce harin ya fara da misalin ƙarfe 1:00 na dare ranar Juma’a, lokacin da ‘yan ta’addan suka kai hari kan sansanin dakarun soji.

Sai dai da gaggawa sojoji suka mayar da martani, tare da samun taimakon jiragen yaki irin su A-29 Super Tucano da Dragon, waɗanda suka yi luguden wuta kan ‘yan ta’addan.

Sojoji sun lalata manyan motocin Boko Haram

Kara karanta wannan

Sojoji, 'yan sanda sama da 30 aka damke suna sayar da makamai ga yan ta'adda

Bayan artabu mai tsanani da ya ɗauki kusan sa’o’i biyu da rabi, rahotanni sun tabbatar da cewa an kashe aƙalla ‘yan ta’adda 60, yayin da aka lalata motoci biyu da ke ɗauke da bindigogi.

Sojojin ƙasa sun kuma fara bin sawun ‘yan ta’addan da suka tsere, inda suka ci gaba da ragargazarsu tare da samun karin nasara a farmakin da ya biyo baya.

Sojoji na cigaba da kai farmaki kan Boko Haram

Zagazola Makama ya wallafa a X cewa wani jami’in tsaro ya shaida masa cewa ana cigaba da kai hari kan 'yan ta'addan, inda dakarun sama ke sake kai wa ragowar ‘yan ta’addan farmaki.

Jami'in ya ce:

“Wannan farmaki yana daga cikin mafi ƙarfi da nasara da muka samu a ‘yan watannin nan.
"Hadin gwiwar sojojin ƙasa da jiragen yaki na da matuƙar tasiri wajen samun wannan nasara,”
Sojoji
Sojoji na cigaba da fatattakar Boko Haram bayan kai musu hari a Borno. Hoto: H Nigerian Army
Source: Facebook

Ana sa ran farmakin zai ƙara rage ƙarfin Boko Haram da ISWAP a yankin, tare da tabbatar da zaman lafiya a Arewa maso Gabas.

'Yan bindiga sun sace mutane 127 a Kebbi

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan bindiga masu garkuwa da mutane sun sace mutane 127 a jihar Kebbi.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gano 'yan kasashen waje na ba Boko Haram horo, an kama mutum 4

Rahotanni sun tabbatar da cewa maharan sun shiga kauyukan jihar Kebbi ne a kan babura dauke da bindigogi.

Baya ga sace mutane 127 din, wasu majiyoyi sun tabbatar da cewa 'yan bindigan sun kashe mutane shida ciki har da mace.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng