Bayan Sanin Makomarsa a Kotu, Gwamnan Edo Ya Aika Sako ga Abokin Hamayyarsa
- Gwamnan Edo, Monday Okpebholo, ya gamsu da hukuncin da kotun ɗaukaka ta yanke kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar
- Sanata Monday Okpebholo ya buƙaci abokin takararsa na jam'iyyar PDP, Asue Ighodalo ya karɓi hukuncin da kotun ta yanke
- Ganin nasararsa, ya bayyana cewa lokaci ya yi da ya kamata a haƙura da zuwa kotu, don a tsaya a yi wa al'ummar jihar aiki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Edo - Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya aika saƙo ga ɗan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen gwamnan da aka gudanar a ranar 21 ga watan Satumba, 2024, Asue Ighodalo.
Gwamna Okphebolo ya yi kira ga Asue Ighodalo da ya karɓi hukuncin da kotun ɗaukaka ƙara ta yanke a ranar Alhamis, wanda ya tabbatar da nasararsa a matsayin gwamna.

Source: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban mai magana da yawun gwamnan, Fred Ituah, ya fitar a ranar Alhamis, 29 ga watan Mayun 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan
PDP ta sha kaye, kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci a ƙarar da aka nemi tsige gwamna
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ɗaukaka ƙara a hukuncin da ta yanke ranar Alhamis, ta sake nazarin hujjojin da ɓangarorin daban-daban suka gabatar, kuma ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe, inda ta tabbatar da sahihancin zaɓen Gwamna Okpebholo.
Me Okpebholo ya ce kan hukuncin kotu
Gwamna Okpebholo ya bayyana hukuncin a matsayin tabbacin ra’ayin jama’a, wanda kuma ya kamata ya zama saƙo mai ƙarfi ga ƴan siyasa, musamman Asue Ighodalo.
"Gwamna Monday Okpebholo na yabawa alƙalai bisa jajircewarsu kan gaskiya da kuma nuna matsayinsu a matsayin inda talaka zai samu adalci."
"Wannan hukunci ba wai kawai nasara ba ce ga jam’iyyarmu ta APC ba, nasara ce ga dimokuraɗiyya a jihar Edo."
"Gwamna Okpebholo ya buƙaci ƴan adawa da Asue Ighodalo da su yi nazari a kan wannan hukunci. Ci gaba da garzayawa kotu ba zai haifar da wani ɗa mai ido ba face ya janye hankali daga aikin mulki da buƙatar kawo ci gaba ga jama’a."
"Gwamnan ya jaddada cewa tun farko ya buɗe kofa ga kowa da kowa ba tare da la’akari da jam’iyyar siyasa ba, yana mai jaddada cewa ci gaban jihar mu ya fi komai muhimmanci. Yana maimaita wannan kira a yanzu."
"Yanzu lokaci ne na rungumar halin kishi da sanin ya kamata. Tsarin shari’a ya kammala, kuma hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ya bayyana ƙarara."
- Fred Ituah

Source: Twitter
Okpebholo zai ci gaba da ayyuka a Edo
Gwamna Okpebholo ya tabbatar wa al’ummar jihar Edo cewa ya tsaya tsayin daka kan manufarsa, wacce ke da nufin kawo saurin ci gaba a fannoni daban-daban kamar ababen more rayuwa, ilmi, lafiya, da kuma ƙarfafa tattalin arziki.
"Gwamnatin Gwamna Okpebholo ta bukaci duk ‘yan jihar da ke da kishin kasa da su kasance cikin nutsuwa tare da ci gaba da harkokinsu na yau da kullum cikin lumana."
- Fred Ituah
Kotu ta shirya yanke hukunci a zaɓen Edo
A wani labarin kuma, kun ji yadda kotun ɗaukaka ƙara da ke zamanta a Abuja ta shirya raba gardama kan shari'ar zaɓen gwamnan jihar Edo.
Kotun za ta yanke hukunci kan ƙarar da Asue Ighodalo na jam'iyyar PDP ya ɗaukaka yana ƙalubalantar nasarar da Gwamna Monday Okpebholo ya samu a zaɓen gwamnan jihar Edo.
Kwamitin alƙalai uku ne zai yanke hukunci a ƙarar, wadda aka nemi a tsige Gwamna Okpebholo na jam'iyyar APC.
Asali: Legit.ng
