Ambaliya: Ana Tsoron Rayuka sama da 50 Sun Salwanta bayan Gano Gawarwaki 15 a Neja

Ambaliya: Ana Tsoron Rayuka sama da 50 Sun Salwanta bayan Gano Gawarwaki 15 a Neja

  • Akalla mutane 50 ne ake zargin sun mutu a mummunar ambaliya da ta afkawa karamar hukumar Mokwa a jihar Neja
  • Shugaban karamar hukumar, Hon. Jibrin Abdullahi Muregi ya shaidawa Legit cewa har yanzu da ake hada rahoton ana aikin ceto
  • Ya ce an samu gawarwaki akalla 15 yayin da hukumomi ke kokarin ganin an samu ceto wasu ko gano karin wadanda suka rasu

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Niger – Mazauna garin Mokwa da ke jihar Neja na cikin halin kakanikayi bayan wata mummunar ambaliya da ta biyo bayan ruwan sama mai karfi da aka ce ta kashe mutum akalla 50.

Wannan ambaliya ta kuma yanke babbar hanyar da ke hade Arewa da Kudancin Najeriya, wacce ke wucewa ta cikin garin Mokwa, lamarin da ya sa jama’a suka shiga cikin rudani.

Kara karanta wannan

2027: Sanatoci sun gano dalilin kara karfin Boko Haram da sauran 'yan ta'adda

Jihar Neja
An samu mummunar ambaliya a Neja Hoto: Niger state/Suleiman Ibrahim
Source: Facebook

Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa har yanzu ba a samu cikakken bayani ba game da asarar da aka yi ba, amma mazauna yankin na ganin adadin mutanen da suka rasa rayukansu zai iya haura 50.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An samu mummunan ambaliya a Neja

A wata tattaunawa ta wayar tarho da Legit ta yi da shugaban karamar hukumar Mokwa, Hon. Jibrin Abdullahi Muregi, ya tabbatar da aukuwar ambaliyar.

Ya ce zuwa yanzu an gano gawarwaki 15, yayin da ake ci gaba da kokarin gano sauran da ambaliyar ta yi gaba da su.

Umar Bago
Ana neman gawarwakin jama'a a Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

Hon. Muregi ya ce:

"Kowanne lokaci muna samun ambaliya a wannan yanki, amma wannan shi ne karon farko da ambaliya ta shafi hedikwatar karamar hukumar Mokwa a irin wannan mummunan yanayi. Har yanzu mutane na kokarin dawowa hayyacinsu."
"Ruwan ya shigo da karfi daga shiyyar Mashegu, ya shiga gidajen mutane, ya lalata su, ya kwashe kayan gida, har da mutane da dama."

Kara karanta wannan

Mutane 2 sun rasu da suka ɗauko ragunan layya da Babbar Sallah a Najeriya

Ana laluben mutane a ambaliyar Neja

Shugaban karamar hukumar ya kara da cewa yanzu haka an fara kokarin samar wa wadanda suka rasa gidajensu mafaka, yayin da ake ci gaba da laluben wadanda ba a gani ba.

Ya ce an fara shirye-shiryen tsugunar da su a makarantun firamare da sakandare da ke yankin, tare da tanadin kayan abinci da sauran tallafi na gaggawa.

Wasu daga cikin mazauna yankin sun bayyana cewa gidaje da kadarori na miliyoyin Naira sun salwantar a ambaliyar.

Sannan wasu sun ce adadin mamatan zai iya haura 50, domin kuwa har yanzu akwai mata da kananan yara da dama da ba a san inda suke ba.

Ambaliya ta yi barna a Kebbi, Neja

A wani labarin, kun ji cewa ibtila’in ambaliyar ruwa ya lalata amfanin gonakin al’umma a karamar hukumar Argungu da sassan jihohin Kebbi da Neja, wanda jefa jama'a a matsala.

Shugaban sashin hulɗa da jama’a na Hukumar Bunƙasa Wutar Lantarki ta Ƙasa (N-HYPPADEC), Nura Wakili ne ya bayyana hakan cikin sanarwa da ya fitar a ranar Talata, 28 ga Mayu, 2025.

Hukumar ta bayyana cewa lalacewar gonaki da ambaliyar ta haifar wani babban koma baya ne ga ƙoƙarin da ake yi na tabbatar da wadatar abinci mai ɗorewa a fadin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng