Talakawa Sun Saya wa Shugaban Gwamnonin Arewa Ragon Layya a Gombe
- Mutanen unguwar Nayinawa a Gombe sun yi karo-karo, sun sayawa Gwamna Inuwa Yahaya ragon layya don nuna godiya
- Rahotanni sun nuna cewa kyautar ta biyo bayan aikin gyaran babban kwari ne da ke hana shiga unguwar lokacin damina
- Dan Majen Nayinawa ya bayyanawa Legit Hausa cewa aikin ya yaye damuwa ga mutanen da suka dade cikin wahala a unguwar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Gombe - Mutanen unguwar Nayinawa da ke cikin birnin Gombe sun shiga murna da godiya bayan gwamna Inuwa Yahaya ya cika alkawarin da ya dade da yi musu.
Alkawarin da gwamnan ya dauka na gyara wani kwari da ke hana shiga unguwar lokacin damina ya jima ba a aiwatar da shi ba, sai dai yanzu gwamnatin jihar ta gyara shi.

Source: Facebook
Mai taimakawa gwamnan a kan harkokin sadarwa, Yusuf Al-Yusra ya wallafa a Facebook cewa gwamnan ya shiga unguwar duba aikin bayan kammala shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A sakamakon wannan aiki, mutanen unguwar suka hadu waje guda suka sayawa gwamna rago domin nuna farin ciki da godiya ga abin da ya yi musu.
Kwarin Nayinawa ya hana walwala shekaru da dama
Kwarin da ke cikin unguwar Nayinawa ya kasance babban kalubale ga mazauna yankin, inda yake hana su zirga-zirga lokacin damina.
A duk lokacin da aka samu ruwan sama, kwarin na cika, yana haifar da cikas ga dalibai, mata da kuma manya wajen shiga unguwar ko fita.
Masu abubuwan hawa da suka hada da babura da Keke Napep na kin shiga unguwar saboda kwarin, musamman a lokacin damuna.

Source: Facebook
A shekarar da ta wuce ne gwamnan jihar ya sanyawa titin da ke kusa da Nayinawa sunan shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje.
An saya wa gwamna Inuwa ragon layya
A lokacin da gwamnan ya kai ziyara domin duba aikin gyaran kwarin, sai jama’ar unguwar suka fito suka ba shi kyautar rago a matsayin alamar godiya.
Wannan mataki ya nuna cewa talakawa na iya yaba da abin alheri idan an yi musu aiki mai amfani ga rayuwarsu.
'Dan Majen Nayinawa ya yi karin bayani
Legit Hausa ta zanta da Dan Majen Nayinawa, Adamu Muhammad Nasir, wanda ya ce mutanen unguwar ne suka hada kudin domin sayo ragon.
Ya bayyana cewa aikin da gwamnan ya yi ya kasance abin da suka dade suna roƙon gwamnati tun shekaru da dama amma bai samu cika ba sai yanzu.
"Yaba kyauta tukwuici," inji 'Dan Majen Nayinawa
A cewar Adamu Muhammad Nasir, yana da kyau a sakawa duk wanda ya yi wani abu mai kyau da alheri.
'Dan Majen Nayinawa ya ce:
"Ka san dama an ce yaba kyauta tukwuici, to mun yi haka ne domin nuna godiya ga gwamnan kan abin da ya mana a Nayinawa."
Nijar ta hana fitar da ragunan layya
A wani rahoton, kun ji cewa kasar Nijar ta hana fitar da ragunan layya Najeriya da wasu kasashen ketare.
Kasar Nijar ta dauki matakin ne domin habaka tattalinta da kuma samar da wadatattun ragunan layya a fadin kasar.
'Yan kasuwa a Najeriya sun bayyana cewa sun fara shiga wasu kasashen kamar Chadi domin sayen dabbobi a bana.
Asali: Legit.ng


