Bayanin da Bola Tinubu Ya Yi wa Najeriya bayan Cika Shekara 2 a kan Mulki

Bayanin da Bola Tinubu Ya Yi wa Najeriya bayan Cika Shekara 2 a kan Mulki

  • Shugaba Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta farfado da tattalin arziki da rage hauhawar farashi bayan tsauraran matakan da aka dauka tun 2023
  • Bola Tinubu ya ce cire tallafin mai da daidaita farashin canjin kudi ne kadai mafita don hana durkushewar Najeriya gaba daya
  • Shugaban kasar ya ce an samu karin masu zuba jari daga waje, kudin shiga ya karu yayin da ya yi magana kan cika shekara biyu a kan mulki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ce Najeriya ta samu gagarumin ci gaba a shekara biyu da suka gabata tun hawansa mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.

A cewarsa, gwamnatinsa ta mayar da hankali kan farfado da tattalin arziki, rage cin hanci, samar da tsaro da kuma inganta walwalar al'umma.

Kara karanta wannan

Atiku ya tono manyan 'kurakuran' Tinubu a shekara 2, ya yi raddi mai zafi

Bola Tinubu
Bola Tinubu ya ce an samu nasara a shekara 2 da ya yi a kan mulki. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Bayo Onanuga ya wallafa a X cewa cire tallafin mai da karya darajar Naira sun takaita barnar da tattalin arzikin Najeriya ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bola Tinubu ya ce a yanzu ana samun saukin hauhawar farashin kaya da kuma karin kudin shiga daga fannonin albarkatu da haraji.

Maganar Tinubu kan cire tallafin mai

Tinubu ya ce cire tallafin man fetur da karya darajar Naira sun taimaka wajen dakile tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya da kuma hana ta durkushewa gaba daya.

Ya ce wadannan matakai sun hana yawaitar bashi da kuma matsin lamba na karancin mai da za su iya kara jefa kasa cikin halaka.

A cewarsa, gwamnati ta dauki wadannan matakai ne saboda yanayi maras kyau da tattalin arzikin kasa ya shiga.

Shugaban ya bayyana cewa sakamakon wadannan gyare-gyare, Najeriya ta samu karin kudin shiga sama da Naira tiriliyan 6 a shekarar 2024.

Tinubu ya ce ya inganta tsaro da tattali

Kara karanta wannan

Tinubu zai kaddamar da manyan ayyuka a Kano da Legas kafin sallar layya

Shugaba Tinubu ya ce ana ci gaba da inganta harkar tsaro ta hanyar hadin guiwa tsakanin jami’an tsaro, da kai hare-hare bisa bayanan sirri.

Ya ce hakan ne ya sa aka fara komawa noma a yankunan da da suka fuskanci matsalar 'yan bindiga musamman a Arewa maso Yamma.

A fannin tattalin arziki, ya bayyana cewa farashin kayan abinci kamar shinkafa ya fara raguwa, hakar mai ya karu da 400%.

Ya ce babban nasarar da aka samu ita ce janye daukar bashi daga Babban Bankin Najeriya (CBN), da kuma gyaran bangaren haraji, wanda ya taimaka wajen kara yawan harajin da ake karba.

Maganar haraji da kula da matasa

Gwamnatin Tinubu ta ce ta aiwatar da gyaran haraji domin saukaka wa talakawa da karfafa kanana da matsakaitan masana’antu.

Shugaban ya ce gwamnati na mai da hankali kan matasa ta hanyar samar da ayyukan yi, tallafin kanana masana’antu, da samar da sababbin fasahohin zamani da za su karfafa harkar kere-kere.

Bangaren lafiya, ilimi da manyan ayyuka

A fannin lafiya, ya ce an gyara fiye da cibiyoyin lafiya matakin farko 1,000, sannan wasu 5,500 na kan hanya.

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya kaddamar da shirin yaki da cutar da yara a Najeriya

Tinubu ya ce an kaddamar da cibiyoyin maganin cutar daji shida, sannan ana bayar da maganin hawan jini da cututtuka masu tsanani kyauta ko da rangwame.

Tinubu
Tinubu ya za a cigaba da ganin amfanin tsare tsarensa a Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnati ta kuma bude tsarin lamunin dalibai don tallafa wa wadanda ba su da galihu su samu damar shiga jami’o’i.

Ya ce ana ci gaba da manyan ayyukan gina hanyoyi kamar Abuja-Kaduna-Kano, Legas-Kalaba, Sokoto-Badagry da sauran su, tare da gyaran layukan wutar lantarki.

Shugaban ya ce lokaci ya yi da za a girbi sakamakon gyare-gyaren da aka yi, yana mai cewa Najeriya tana kan hanya madaidaiciya zuwa ci gaba mai dorewa.

Tinubu ya nada mukamai a manyan makarantu

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da nada mutane 61 a manyan makaratu.

An fitar da sunayen mutanen ne a ranar Laraba yayin da aka fara murnar cika shekara biyu a kan karaga da Tinubu ya yi.

Legit ta rahoto cewa mutane 61 sun samu mukamai ne a manyan makarantun tarayya 36 da ke Arewaci da Kudancin kasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng