Tinubu zai Kaddamar da Manyan Ayyuka a Kano da Legas kafin Sallar Layya

Tinubu zai Kaddamar da Manyan Ayyuka a Kano da Legas kafin Sallar Layya

  • Shugaba Bola Tinubu ya isa birnin Legas domin halartar shagulgulan cikar shekara 50 da kafa kungiyar kasashe Yammacin Afrika ta ECOWAS
  • Ziyarar ta haɗa da kaddamar da manyan ayyuka da suka kunshi titin gabar teku na Legas zuwa Calabar da hanyar tashar jiragen ruwa ta Lekki
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa Tinubu zai kaddamar da wasu ayyuka a Kano kuma zai yi bukukuwan sallah a Legas kafin ya koma Abuja

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya sauka a birnin Legas domin halartar wasu muhimman taruka da kuma kaddamar da manyan ayyukan raya ƙasa.

Ziyarar ta shugaba Tinubu na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke shirye-shiryen shagulgulan babbar sallah da kuma bikin cikar kungiyar ECOWAS shekaru 50 da kafuwa.

Kara karanta wannan

Abu ya girma: Sanata ya halarci zaman majalisar dattawa sanye da rigar Tinubu

Bola Tinubu
Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Legas. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Legit ta tattaro bayanai kan ziyarar shugaban kasar ne a cikin wani sako da mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya wallafa a Facebook.

A filin jirgin saman Murtala Muhammed ne Gwamnan Jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu da mataimakinsa, Obafemi Hamzat, suka tarbe shi da sauran jami’ai.

Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Legas

Tinubu zai kaddamar da Sashe na I na titin gabar teku daga Legas zuwa Calabar, wanda ke daga cikin manyan ayyukan da ke da nufin bunƙasa zirga-zirga da tattalin arziki a Kudu.

Hakanan, Shugaban Najeriyan zai kaddamar da hanyar tashar jiragen ruwa ta Lekki, tare da kaddamar da Sashe na II na titin Legas-Calabar da kuma hanyar 7th Axial Road.

Tinubu zai kaddamar da ayyuka a Kano

Baya ga kaddamar da ayyuka a Legas, Tinubu zai yi amfani da fasahar zamani domin kaddamar da wasu ayyuka a jihohi kamar Kano da Katsina ta amfani da yanar gizo.

Kara karanta wannan

Hajjin bana: Mahajjaciyar Najeriya ta rasu a asibitin Makkah

Ayyukan sun hada da hanyar Kano-Kanwar-Danja-Hadejiya Sashe na II, Yakasai-Zalli, da kuma buɗe hanyar Kano Northern By-pass.

Sauran hanyoyin sun haɗa da Zaria-Hunkuyi-Dabai Sashe na I, Dabai-Kafur-Malumfashi, da Malumfashi-Dayi-Yashe-Gidan Mutum Daya Sashe na III.

Tinubu
Tinubu zai bude ayyuka a Kano ta yanar gizo. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Tinubu zai jagoranci taron ECOWAS a Legas

A matsayinsa na shugaban ƙungiyar ECOWAS, Tinubu zai jagoranci bikin cika shekara 50 da kafuwar ƙungiyar da za a gudanar a cibiyar harkokin ƙasashen waje ta Najeriya.

Bikin zai haɗa manyan shugabannin ƙasashen yammacin Afirka, masu ruwa da tsaki da sauran baki domin nazarin ci gaban da ECOWAS ta samu da kuma tsara hanyoyin cigaba a gaba.

Rahoton AIT ya nuna cewa bayan kammala tarurruka da shagulgula, ana sa ran Tinubu zai yi bukukuwan sallah a Barikin Dodan kafin ya koma babban birnin tarayya Abuja.

Bola Tinubu zai ci bashi daga ketare

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nemi izinin majalisa wajen ciwo bashin dala miliyan 21.1 da wasu karin kudi.

Ana hasashen cewa bashin da shugaban kasan ke shirin ciwo wa domin yin wasu ayyuka zai haura Naira tiriliyan 30.

Shugaban kasa Tinubu ya ce karbo rancen kudin zai taimaka wajen cike gibin da aka samu a Najeriya bayan cire tallafin man fetur.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng