Tinubu zai Kinkimo Bashin Dala Biliyan 21.1 domin Wasu Ayyuka a Najeriya
- Shugaba Bola Tinubu ya aika da wasiƙa zuwa Majalisar Wakilai yana neman amincewa da shirin neman bashi na $21.5bn daga ƙasashen waje
- Haka kuma, ya buƙaci izinin samun rance daga cikin gida na ₦757.9bn domin biyan bashin fanshon da ma'aikata ke bin da gwamnati
- Tinubu ya ce bashin zai taimaka wajen magance gibin kuɗi da ɗaura ƙasa kan tubalin ci gaba, musamman bayan cire tallafin mai
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tura wasiƙa zuwa ga Majalisar Wakilai domin neman amincewa da sabuwar hanyar karbo bashi daga ƙasashen waje.
Tinubu ya bayyana cewa sabon shirin karbar bashin da ya shafi shekarar 2025 zuwa 2026 zai ƙunshi manyan sassa daban-daban na tattalin arzikin ƙasa.

Source: Facebook
Vanguard ta wallafa cewa ayyukan da bashin zai shafa sun haɗa da fannin noma, lafiya, ilimi, ruwa, tsaro da kuma samar da ayyukan yi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ayyukan da Bola Tinubu zai yi da bashin
Shugaban ya ce dalilin neman bashin ya samo asali ne daga ƙarancin kuɗi a cikin gida da kuma gibin da aka samu sakamakon cire tallafin mai da yake da tasiri ga rayuwar al’umma.
Tinubu ya ƙara da cewa za a mayar da hankalin kan manyan ayyukan raya ƙasa kamar layin dogo, asibitoci, da kawo ci gaba a dukkan jihohi 36 da babban birnin tarayya.
Business Day ta wallafa cewa shugaban kasar ya ce:
“Wannan shiri zai haifar da ayyukan yi, koyar da sana’o’i, rage talauci, da tabbatar da wadatar abinci, da inganta rayuwar ‘yan Najeriya.”
Tinubu ya nemi kuɗi domin biyan 'yan fansho
A wani ɓangare daban, Tinubu ya nemi amincewar Majalisar domin karbar lamuni na gida da ya kai ₦757,983,246,572 domin biyan bashin 'yan fansho.

Kara karanta wannan
"An talauta 'yan Najeriya": Tsohon ministan Buhari ya yi raga raga da gwamnatin Tinubu
Ya ce gwamnati ta kasa biyan wasu hakkokin 'yan fansho na shekarun baya saboda ƙalubalen samun kuɗin shiga, wanda hakan ya jefa masu ritaya cikin mawuyacin hali.
Tinubu ya bayyana cewa Majalisar Zartaswa ta tarayya ta riga ta amince da wannan shiri tun a zaman ta na ranar 4 ga Fabrairu, 2025.
Batun farfaɗo da biyan 'yan fansho
A cewarsa, biyan bashin fansho zai dawo da amincewa da tsarin, ya inganta rayuwar tsoffafin ma’aikata, da kuma karfafa tattalin arzikin ƙasa.
Tinubu ya ce hakan zai sa gwamnatin tarayya ta cika wajibinta na biyan 'yan fansho, kuma zai rage radadin rayuwa ga tsofaffin ma’aikata tare da basu damar biyan bukatun rayuwarsu.
Tinubu zai inganta rayuwar yara a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi alkawarin cigaba da inganta rayuwar yara.
Shugaban kasar ya yi magana ne yayin da ya ke taya yaran Najeriya murnar ranar yara ta duniya a yau, 27 ga Mayu.
Bola Tinubu ya bayyana cewa ya kaddamar da shiri na musamman domin yaki da cin zarafin yara kanana a Najeriya.
Asali: Legit.ng
