Gwamna Bago Ya Tono Abubuwa 2 da ke Ƙara Ta'azzara Matsalar Tsaro a Najeriya

Gwamna Bago Ya Tono Abubuwa 2 da ke Ƙara Ta'azzara Matsalar Tsaro a Najeriya

  • Gwamna Umaru Bago na jihar Neja ya bayyana cewa talauci da jahilci ne tushen matsalar tsaron da ke addabar al'umma a Najeriya
  • Bago ya bukaci a ɗauki matakai da gaggawa domin ilimantar da jama'a da fitar da su daga ƙangin talauci da kuncin da suke ciki
  • Gwamnan ya faɗi haka ne da ya karɓi bakuncin tawagar masu karatun kwas din harkokin leken asiri waɗanda ke rangadi a jihar Neja

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bayyana cewa talauci da jahilci ne ke kara rura wutar rashin tsaro a kasar nan.

Gwamna Bago ya faɗi hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar mutane 13 na “Syndicate 5” masu halartar kwas din harkokin leken asiri a Cibiyar Nazarin Tsaro ta Kasa da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya fadi sirrin kawo karshen zubar da jini a Kaduna

Gwamna Bago.
Gwamna Bago na jihar Neja ya ce jahilci da talauci ne ke ƙara rura wutar matsalar tsaro a Najeriya Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

Rahoton jaridar Leadership ya nuna cewa tawagar, wadanda ke rangadi a jihar Neja ta ziyarci Gwamna Umaru Bago a gidan gwamnatinsa da ke Minna.

Abubuwa 2 da ke rura wutar matsalar tsaro

Yayin da yake kira da a dauki matakai na musamman don magance matsalolin talauci da jahilci a cikin al’umma, Gwamna Bago ya ce:

“Talauci da jahilci su ne tushen matsalolin rashin tsaron da suka addabi ƙasar nan.”

Saboda haka, gwamnan ya bukaci a dauki matakai masu karfi kuma cikin gaggawa don dakile wannan mummunan lamari da ke jawo asarar rayuka a Najeriya.

Umaru Bago ya yaba da matakin da cibiyar ta ɗauka na zaɓen jihar Neja a matsayin daya daga cikin wuraren da tawagar za ta kai ziyara.

Wane mataki Gwamna Bago ya ɗauka a Neja?

Ya ce wannan mataki ne mai kyau kasancewar jihar Neja na ɗaya daga cikin jihohin da matsalar tsaro ta shafa a Arewacin Najeriya rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Turji ya zafafa hare-hare a Sakkwato, mazauna kauyuka 20 sun fara kaura

A cewarsa, gwamnatin jihar Neja na kokarin ilmantar da al’ummarta don su fita daga kangin talauci, ta hanyar amfani da dimbin albarkatun kasa da sauran damarmaki da ake da su.

Gwamna Bago ya nuna kwarin gwiwa cewa binciken da tawagar za ta yi zai taimaka wa gwamnatoci a matakai daban-daban wajen tsara sababbin dabarun tabbatar da tsaro.

Gwamna Bago.
Gwamna Bago ya buƙaci gwamnatin tarayya ta magance talauci da jahilci don dawo da tsaro a ƙasar nan Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Facebook

A nasa jawabin, shugaban tawagar, R.A. Bolarinwa, ya bayyana cewa mambobin “Syndicate 5” guda 13 na daga cikin mahalarta kwas din EIMC 18 da suka kai 78 a fadin kasar nan.

Ya ce an kafa tawagar ne domin horar da shugabanni da masu ruwa da tsaki a harkar tsaro kan ilimin da ya dace wajen tunkarar kalubalen tsaro masu sarƙaƙiya a hukumominsu.

Gwamna Bago ya taiƙaita zirga-zirga a Minna

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umaru Bago ya hana zirga-zirgar Keke Napep da babura daga ƙarfe 6:00 na yamma zuwa 6:00 na safe a Minna, babban birnin Neja.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ke saboda ƙaruwar matsalar tsaro da aikata miyagun laifuffuka, ya ce hanin na ɗan lokaci ne.

Umaru Bago ya jaddada cewa gwamnatinsa ba za ta zuba ido ta ƙyale yagu su ci gaba da tada zaune tsaye ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: