Tinubu Zai Gana da Kamfanonin Samar da Lantarki da Aka Fara Zancen Karin Kudi

Tinubu Zai Gana da Kamfanonin Samar da Lantarki da Aka Fara Zancen Karin Kudi

  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya shirya kawo ƙarshen matsalolin da suka addabi ɓangaren samar da lantarki na ƙasar nan
  • Mai girma Bola Tinubu zai gana da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki na Najeriya
  • Ganawar ta su ba ta rasa nasaba da samo hanyoyin da za a bi domin magance matsalolin da suka addabi samar da lantarki a ƙasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ana sa ran shugaban Ƙasa Bola Tinubu zai gana da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki a Najeriya.

Ganawar Shugaba Tinubu da shugabannin kamfanonin na daga cikin matakan gaggawa da ake ɗauka don nufin magance bashin N4trn da ke barazanar durƙusar da tsarin rarraba wutar lantarki a ƙasar nan.

Bola Tinubu da Adebayo Adelabu
Tinubu zai yi zama da shugabannin kamfanonin samar da lantarki na Najeriya Hoto: @DOlusegun, @BayoAdelabu
Source: Twitter

Wannan mataki ya biyo bayan wata ganawa ta manyan jami'ai da aka yi ranar Talata tsakanin ministan lantarki, Adebayo Adelabu, da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki a birnin Abuja, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Hadakar Atiku ta fara gigita APC, an fallasa abin da Tinubu ke kullawa 'yan adawa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ɓangaren samar da lantarki na fama da matsaloli

An yi ganawar ne sakamakon fargabar yiwuwar rugujewar turken rarraba wutar lantarki na ƙasa saboda rashin isasshen kuɗi a ɓangaren, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar wuta ta bayyana a ranar Lahadi.

Gwamnatin tarayya ta yi alƙawarin ɗaukar matakan gaggawa don rage bashin N4trn da kamfanonin samar da wutar lantarki ke bin ta.

A baya kamfanonin samar da wutar lantarki sun yi gargaɗi ga gwamnatin tarayya dangane da ci gaba da tara bashi da ya haura N4trn.

Kamfanonin sun bayyana cewa suna bin bashin N2trn dangane da wutar da suka samar a shekarar 2024, tare da N1.9trn na tsofaffin basussuka.

A cewar sanarwar mai ba ministan shawara na musamman kan harkokin sadarwa da hulɗar da jama'a, Bolaji Tunji, gwamnatin tarayya ta yanke shawarar biyan wani kaso mai yawa na bashin nan take.

Sanarwar ta ce za a biya ragowar ta hanyar amfani da takardun alƙawarin biyan bashi a cikin watanni shida masu zuwa.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun yi artabu da mafarauta a Sokoto, an samu asarar rayuka

Bola Tinubu zai gana da shugabannin GenCos

Ya bayyana cewa wannan shawarar za ta kasance ɗaya daga cikin abubuwan da za a tattauna yayin taron da ake shiryawa tsakanin Shugaba Bola Tinubu da shugabannin kamfanonin samar da wutar lantarki.

Ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na da niyyar hana rugujewar ɓangaren samar da wutar lantarki, yana bayyana lamarin a matsayin wani abin gaggawa da ya shafi ƙasa.

"Mun fahimci cewa wannan lamari yana buƙatar ɗaukar matakan gaggawa. Gwamnati na da niyyar warware wannan bashi domin daidaita ɓangaren da hana ƙarin rikici."

- Bolaji Tunji

Da aka tambaye shi kan ranar da za a yi taron, mai taimakawa ministan ya ce ba zai iya cewa ga lokaci ba a yanzu, amma tattaunawa na ci gaba da gudana tsakanin masu ruwa da tsaki.

Mataimakin gwamna ya koka da tsadar lantarki

A wani labarin kuma, kun ji cewa mataimakin gwamnan jihar Legas, Obafemi Hamzat, ya koka kan tsadar kuɗin lantarki.

Kara karanta wannan

Dakarun sojoji sun yi wa 'yan bindiga kwanton bauna, an samu nasara kan miyagu

Obafemi Hamzat ya nuna damuwarsa kan abin da ya kira aringizon kuɗin wuta da kamfanonin rarraba lantarki suke yi.

Mataimakin gwamnan ya bayyana cewa a watan Afirilu an turo masa kuɗin wata na N29m, saɓanin N2.7m da aka tura masa a watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng